Karatun Ilimi
Majalisar dattawan Najeriya ta nemi gwamnati ta dauki tsattsauran mataki kan iyayen dake barin yaransu na gararanba a kan titi maimakon zuwa makaranta.
Hukumomi a Jami'ar jihar Lagos sun yi martani bayan samun satifiket na digiri a hannun masu siyar da nama a jihar inda suka ce an dade da daukar mataki kan lamarin.
Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umar Bago ya tallafawa dalibai da ke karatu a Jami'ar Abdulkadir Kure da ke jihar inda ya rage kaso 50 na kuɗin da suke biya.
Wani mahaifi mai suna Muhammada Jimeta ya daki malam mai suna Sekinat Adedeji a makarantar Aces a Abuja saboda ta daki yar sa mai suna Karima Muhammad Jimeta.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya yara da iyayensu murna a yayin bikin ranar yara ta duniya ta shekarar 2024. Shugaban ya yi alkawarin ingnata ilimi da tsaro.
Shirin gwamnatin tarayya na tallafawa marasa galihu a kasar nan da bashin ilimi ta gindaya sharuddan da sai an cika su za a samu damar karbar rance.
Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin da zai binciki dalilin da ya janyo daliban makarantun sakandiren jihar nan suka yi mummunar faduwa a jarrabawar 'qualifying'.
Gwamnatin jihar Kwara ta ce akalla almajirai 158 ne gwamnatin jihar Kwara ta kwashe daga titunan Ilorin tare da mayar da su jihohinsu a cikin shekara daya.
Iyayen yara a jihar Oyo za su shiga wani hali bayan shugaban makarantar da yaransu ke zuwa ya cika wandonsa da iska da kudin jarrabawar kammala sakandare.
Karatun Ilimi
Samu kari