Halin Kunci: Gwamnan APC Ya Tabo Daliban Firamare, Ya Raba Musu Kyautar N10,000 Domin Rage Radadi

Halin Kunci: Gwamnan APC Ya Tabo Daliban Firamare, Ya Raba Musu Kyautar N10,000 Domin Rage Radadi

  • Daliban firamare da sakandare a jihar Ogun sun jike da kudi bayan Gwamna Dapo Abiodun ya gwangwaje su da kyautar N10,000 kowannensu
  • Akalla dalibai 100,000 ne za su ci gajiyar kyautar N10,000 da gwamna ke yi da ke makarantun gwamnati 2,000 domin rage musu halin kunci
  • Gwamnatin jihar ta bayyana haka ne a shafinta na X a yau Alhamis 14 ga watan Maris inda ta ce wannan mataki zai taimakawa daliban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun – Gwamnatin jihar Ogun ta fara rabon kudi N10,000 ga daliban firamare da sakandare saboda halin kunci da ake ciki.

Gwamna Dapo Abiodun ya ce akalla dalibai 100,000 za su ci wannan gajiya ta kyautar kudin a makarantun gwamnati guda 2,000 a jihar.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Gwamnan APC zai rage farashin kayan abinci da 25% yayin da aka fara azumi

Gwamna ya gwangwaje daliban firamare da kyautar N10,000 ga kowannensu
Gwamna Abiodun ya raba kudin ne ga daliban domin rage musu halin kunci. Hoto: Dapo Abiodun.
Asali: Twitter

Dalilin Gwamna Abiodun na biyan dalibai N10, 000

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na X a yau Alhamis 14 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dapo Abiodun ya dauki matakin ne domin tallafawa dalibai marasa karfi da ke karatu a makarantun gwamnati a Ogun.

Yayin kula da yadda rabon ke tafiya, Kwamishinan ilimi a jihar, Farfesa Arigbabu Abayomi ya bayyana himmatuwar gwamnatin jihar domin rage wahalhalu a jihar.

“Gwamnati ta dauki matakai ta hanyoyi da dama domin dakile wahalhalun da ake ciki musamman al’ummar jihar.”
“Ta fannin ilimi, muna ba da tallafin N10,000 ga daliban firamare da sakandare 100,000 a fadin jihar.”

- Farfesa Arigbabu Abayomi

Yadda rabon N10, 000 ya kasance a Ogun

Farfesan ya ce su na yin rabon kudaden ne ta hannun iyayen daliban kasancewar yaran ba su da asusun bankuna.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamnan APC ya ware N6.7bn domin rabawa marayu da talakawa tallafin azumi

Kwamishinan yake cewa matakin da Gwamna Abiodun ya dauka zai taimakawa iyayen wurin sauke nauyin kula da ‘ya’yansu musamman ta fannin ilimi.

Gwamna Sanwo-Olu zai rage farashin kaya

Kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya dauki matakin rage farashin kayan abinci a jihar.

Sanwo-Olu ya tabbatar da himmatuwar gwamnatinsa wurin rage farashin kaya musamman abinci da kaso 25 yayin da ake fama.

Wannan matakin na zuwa yayin da aka shiga watan Ramadan a cikin wani irin yanayi na kunci da tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel