An Bayyana Jami’a 1 a Najeriya da Mata Ke Kammala Karatu da Budurcinsu, Akwai Dalili

An Bayyana Jami’a 1 a Najeriya da Mata Ke Kammala Karatu da Budurcinsu, Akwai Dalili

  • Rabaran Emmanuel Edeh wanda shi ne shugaban Jami'ar Madonna ya bugi kirji kan irin tarbiya da suke bayarwa a makarantar
  • Rabaran din ya ce a Jami'ar ce kaɗai mata ke shiga da budurcinsu su kammala makarantar ba tare da rasa budurcin ba
  • Edeh ya ce hakan bai rasa nasaba da irin bin dokoki da kuma tabbatar da tarbiya mai karfi kan dalibai domin zama nagartattu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Mamallakin Jami'ar Madonna Najeriya, Rabaran Emmanuel Edeh ya bugi kirji kan yadda suke da tarbiya a Jami'ar.

Edeh ya ce a Jami'ar ce kawai 'yan mata da suka samu gurbin karatu da budurcinsu suk kammala karatu ba tare da rasa budurcinsu ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: Tsohon Sanata ya fadi hanyar kawo karshen matsalar tsaro har abada

Jami'ar da 'yan mata ke kammala karatu da budurcinsu
Shugaban Jami'ar Madonna ya ce a makarantar ce kadai mata ke kammala karatu da budurcinsu. Hoto: Emmanuel Edeh, Madonna University.
Asali: Facebook

Dalilin da yasa matan ke kare budurcinsu

Rabaran din ya ce hakan na da nasaba da irin tarbiya da suka dora makarantar a kai da kuma tsantseni kan bin dokoki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Emmanuel ya bayyana haka a yau Laraba 20 ga watan Maris yayin hira da gidan talabijin na Channels.

Ya ce kowa ya sani a Najeriya Jami'ar ta sanu wurin ba da tarbiya da kuma bin dokoki domin samun nagartattun mutane.

Ya kara da cewa mutane da dama daga kasashen ketare su na zuwa Jami'ar Madonna domin neman 'yan matan da ba su rasa budurcinsu ba za su aure.

Martanin Edeh kan Jami'ar Madonna

"A wannan Jami'a ce kadai za ka ga mace da shiga da budurcinta ta kammala ba tare da ta rasa shi ba."
"Ku fada mani wata Jami'a a duniya da ta ke da irin wannan tarbiya, wasu daga Landan da Amurka da Burtaniya su na cewa a Madonna ne kawai ake samun mata da budurcinsu."

Kara karanta wannan

Abin da majalisar dattawa ta buƙaci Tinubu ya yi wa iyalan sojojin da aka kashe a Delta

"Su na cewa su na son auren 'yan mata masu budurci a tare da su, sun sani babu inda za su samu haka sai a Madonna."

- Emmanuel Edeh

Jaruma ta bada shawarar rasa budurci

Kun ji cewa wata jarumar fina-finai ta shawarci ma'aurata su san juna kafin yin aure saboda sanin matsalolinsu.

Jaruma Tosin Adekinsola ta ce hakan ne kadai zai ba su damar sanin ko za su iya ci gaba da zama bayan aure ko kuma akwai matsala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel