Yan Sanda Sun Kama Malamin Jami’a Da Zargin Aikata Babban Laifi a Jihar Yobe

Yan Sanda Sun Kama Malamin Jami’a Da Zargin Aikata Babban Laifi a Jihar Yobe

  • Rundunar ‘yan sanda ta kama wani malamin jami'ar kwalejin kimiyya da fasaha da ke Potiskum, jihar Yobe kan zargin lalata da dalibai
  • Akalla dalibai hudu ne aka yi zargin Mista Adamu Garba Hudu ya yi lalata da su da zimmar zai ba su maki a jarabawa don tsallake darasinsa
  • A wannan karon, an kama Mista Hudu bayan ya yi lalata da wata diliba a ofishinsa da ke babban asibitin jihar Yobe da ke Potiskum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Potiskum, jihar Yobe - Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta kama Mista Adamu Garba Hudu, malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta Al-Ma’arif da ke Potiskum.

An kama Hudu ne a makarantar mai zaman kanta da ke karamar hukumar Potiskum ta jihar Yobe bisa zargin aikata laifin lalata da dalibai.

Kara karanta wannan

'Yan kabilar Igbo masu kasuwanci a jihar Arewa sun koka kan yadda ake karbar haraji a hannunsu

An kamala malamin jami'a yana lalata da dalibai a Yobe
Yan sanda sun ce suna kan gudanar da bincike a kan malamin. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Laifin da Mista Hudu ya aikata

Malamin da aka kama ma’aikaci ne a babban asibitin jihar da ke Potiskum, kuma malami (mai ziyara) a makarantar Al-Ma’arif, inda wadanda abin ya shafa ke karatu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta gano an kama malamin ne bayan da ake zargin ya yi lalata da daya daga cikin dalibansa da kuma yadda ya ke yaudarar daliban da zummar ba su maki.

A wannan karon, an kama Mista Hudu bayan ya yi lalata da wata diliba a ofishinsa da ke babban asibitin.

Abin da rundunar 'yan sanda ta ce

Radio Nigeria ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem ya ce ‘yan sandan sun kama wanda ake zargin ne a ranar Talata.

DSP Abdulkareem ya ce an kama wanda ake zargin ne bisa zargin ‘lalata, cin zarafi da cin amana kuma ana ci gaba da bincike’.

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta nemi a kame dan fafutukar raba Najeriya gida biyu

Ya kara da cewa akalla dalibai hudu a makarantar ne wadanda ya yi lalata da su inda ya ce wanda ake zargin yana da aikata lalata don ba da maki.

Ogun: An kama matashi da ya kashe 'yan mata 7

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta kama wani matashi mai suna Adebayo Azeez bisa laifin kashe 'yan mata bakwai don yin tsafi.

An ruwaito cewa Azeez yana amfani da wani dandalin soyayya da ke a yanar gizo yana yaudarar 'yan matan zuwa gidansa, inda ya ke hada kai da wani malamin tsubbu yana kashe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel