A Karon Farko, An Kaddamar da Al-Kur’ani na Musamman Domin Kurame a Najeriya

A Karon Farko, An Kaddamar da Al-Kur’ani na Musamman Domin Kurame a Najeriya

  • Kungiyar Al-Furkan da wata takwararta a Najeriya sun hada-kai an kaddamar da Kur’ani domin kurame a Najeriya
  • Ustaz Yasir Sulaiman Kofa ya jagoranci wannan aiki wanda aka shafe har kwanaki bakwai ana yi a garin Zariya
  • Malamin makarantar ya ce a sanadiyyar haka, kurame da ke da matsalar ji sun samu damar karanta littafi mai tsarki

Kaduna - Hadaddiyar kungiyar kurame mai suna Al-Furkan da wata kungiya a Saudi Arabiya sun kaddamar da kur’ani domin kurame.

Legit ta samu labari an shirya taron mako guda a jihar Kaduna inda aka kaddamar da littafin Al-Kur’ani mai tsarki da yaren kurame.

Kur'ani
An kaddamar da Kur'anin kurame a Zariya Hoto: Legit
Asali: Original

Wannan kungiya ta kasa watau Al-Furkan ta fara wannan gagarumin aiki a garin Zariya daga ranar Talata, 26 ga watan Disamba 2023.

A babban dakin taro da ke makarantar Barewa College a Zariya aka yi taron wanda ya samu gayyatar manyan sarakuna da malamai.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izala ta yi martani kan hallaka malamin musulunci, ta tura sakon gargadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan da aka gayyata wajen taron

Mai martaba Sarkin Zazzau, Amb. Ahmad Nuhu Bamalli shi ne uban taro, sai Gwamna Uba Sani a matsayin bako na musamman.

Kamar yadda sanarwa ta zo mana, Fagacin Zazzau yana cikin masu kaddamar da Kur’anin bayan an koyawa kuramen yadda ake karatun.

Daga cikin malaman da aka gayyata zuwa wajen taron kaddamarwar akwai Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya da Sheikh Ahmad Gumi.

Al-Furqan za ta taimakawa Kurame

Yasir Sulaiman Kofa ya jagoranci wannan shiri, ya ce sun samu wasu Bayin Allah da su ka dauki dawainiyar wallafa wadannan Kur’anai.

Da Legit ta tuntubi Ustaz Yasir Kofa, ya nuna wannan babban cigaba ne aka samu, ya ce hanyoyi biyu ake bi a karanta littafin mai tsarki.

Kuramen za su iya yin nuni da yarensu ko kuma su rika zayyano harufan Kur’anin da larabci a maimakon su rika bin fassarar Ingilishi

Kara karanta wannan

Bashin dalibai: Tinubu ya bayyana ranar da zai kaddamar da shirin ba dalibai rancen kudi

Kurame da Al-Kur'ani

"Tabbas wannan abu ne wanda zai taimaki kurame, sun dade suna nema.
A wajen akwai wata tsohuwa wanda ta ce duk tsawon shekaru 50 da su ka wuce, fassarar Al-Kur’ani take karantawa.
Amma ka ga yanzu da zuwanta, har ta hardace suratul Fatiha kuma ta fara hardace wasu surori cikin Al-kur’ani.

- Yasir Sulaiman Kofa

Nakasassu za su je karatu a kasar waje

A shekarar da ta gabata ne rahoto ya zo cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta tura har da nakasassu daga Kano zuwa jami’o’in waje.

Kwamishinan ilmi, Umar Haruna Doguwa ne ya yi wa masu nakasa wannan albashiri a madadin gwamna watau Abba Gida Gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel