Addinin Musulunci da Kiristanci
Fafaroma Francis ya rasu bayan fama da cutar numfashi da ya yi a Vatican. Fafaroma Francis ya bukaci a masa jana'iza mai sauki domin nuna shi bawan Allah ne.
Fasto Tunde Bakare ya shawarci Shugaba Tinubu ya rungumi tawali’u da karɓar shawara domin ceto Najeriya daga halin da take ciki inda ya ce an gaji da addu'a.
Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna Fasto David Ibiyeomie yana cewa Annabi Isa bai taba ziyartar talaka ba, yana kin talauci lokacin da yake raye.
Sheikh Sheikh Sulaiman Faruq Onikijipa daga Kwara ya bukaci Olusegun Obasanjo ya karɓi Musulunci saboda irin gudummawar da ya bayar wajen gina masallatai.
Malamin Musulunci a Kano, Sheikh Adam Abdallah Kano ya yi ruwan addu'o'i ga kungiyar ECOWAS da masu goyon bayanta kan dokar batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Juma'a da Litinin a matsayin ranakun hutu domin bikin Easter da Good Friday na 2025. An bukaci Kiristoci su yi wa kasa addu'a.
Gwamnatin Benue ta ware hutun Easter daga Alhamis zuwa Litinin, domin ma’aikata su huta, su yi ibada da kasancewa da iyalai kafin komawa aiki ranar Talata.
A Kaduna, 'yan bindiga sun sace Fasto Samson Ndah Ali daga gidansa a Mararaba Abro. Sojoji da 'yan sanda sun bi sahun wadanda suka yi garkuwa da shi.
Rundunar ‘yan sanda a Gombe ta nesanta kanta daga zargin malamin Musulunci, Sheikh Adam Muhammad Albany kan kisan wani matashi a azumin watan Ramadan.
Addinin Musulunci da Kiristanci
Samu kari