“Ya Ki Ya Sumbace Ta”: Ango Ya Kunyatar da Amaryarsa a Gaban Jama’a a Wajen Daurin Aure

“Ya Ki Ya Sumbace Ta”: Ango Ya Kunyatar da Amaryarsa a Gaban Jama’a a Wajen Daurin Aure

  • A mafi akasarin taron daurin aure, a kan nemi ango da amarya su sumbaci juna, sai dai wani ango ya ki karbar wannan al'adar
  • A lokacin daurin aurensa, mutane sun cika da mamakin yadda angon ya ki sumbatar amaryarsa, abin da ya jawo cece-kuce ga mahalarta taron
  • Mutane da yawa sun yi wa angon dariya suna ganin yana jin kunya ne kawai, yayin da wasu ke mamakin dalilinsa na kunyatar da amaryar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wani faifan bidiyo ya nuna lokacin da wani ango ya ki sumbatar amaryarsa a lokacin daurin aurensu, wanda ya jawo cece-kuce ga mahalarta taron.

Mutane sun yi martani kan angon da ya ki sumbatar amaryarsa
Angon ya bayyana a fili yana jin kunya mutane sosai. A kula: Hoton da ke hannun dama an saka domin misali ne kawai. Hoto: Tim Robberts, Facebook/Zambia News Yathu Media
Asali: Getty Images

Faifan bidiyon wanda kafar yada labarai ta Yathu Media News ta kasar Zambiya ta wallafa an yi masa take da:

Kara karanta wannan

Mun dauki matakan saukar da farashin gas, cewar ministan mai

"Ango ya kunyata amarya ta hanyar kin sumbantar ta a lokacin daurin aurensu acoci."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ango ya kunyata amaryarsa

A cikin faifan bidiyon, amaryar ta durkusa tana kokarin sumbatar ango amma ya rika zulle mata.Wani mutum daga bayan fage ya nemi ta da ta sake gwadawa amma abin dai ci tura.

Hakan ya jefa mahalarta taron cikin mamaki yayin da mutane ke yiwa angon dariya. Amarya ta yi mamaki matuka wanda ya har ta kasa tashi daga inda ta durkusa gabansa.

Ya dai bayyana a fili, angon yana jin kunyar sumbatar amayaryar a gaban taron jama'ar.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Halayen angon: Ra'ayoyi sun banbanta

Somiah Ng'andu Music Ministry ta ce:

"Da alama sha'awarsa ta motsa ne don haka yake jin tsoron fara wasan a gaban kowa."

Kara karanta wannan

Namiji ko mace: Bobrisky ya bayyana ainihin jinsinsa a gaban alkali

Yvonne Chibwe ta ce:

"Yana da kunya sosai."

Morris Mans ya ce:

"Irin wannan mutumin mai kunya, da alama ya ɗauki wani ya ba shi wajen neman auren amaryar saboda ba zai iya yi ba."

Sharon Musonda Mutale ta ce:

"Ki bar shi kawai mu gani idan kun koma gida za ku yi hakan, a nan za a gane ko ganin mutane ne ya sa shi jin kunya."

An gwangwaje amarya da kayan daki

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito yadda wani dangi suka hada wa 'yar uwarsu da za ta yi aure sha tara ta arziki, wanda bidiyon kayan ya jawo magana a soshiyar midiya.

Yayin da wasu ke jinjinawa kokarin dangin na fitar da amaryar daga kunya, wasu kuma na ganin ba abin a baya bane, tunda kamar wajibi ne yi wa amarya kayan daki musamman a Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel