Aure Mai Dadi: Mawaki Davido ya Gwangwaje Amaryarsa da Kyautar Motar Alfarma

Aure Mai Dadi: Mawaki Davido ya Gwangwaje Amaryarsa da Kyautar Motar Alfarma

  • Fitaccen mawaki kuma sabon ango, David Adeleke da aka fi sani da Davido ya gwangwaje amaryarsa da kasaitacciyar mota jim kadan bayan daura aurensu a jihar Legas
  • Hamshakan ‘yan Najeriya ne su ka halarci taron bikin da ya gudana cikin kayatarwa, daga wadanda aka hango a bikin akwai tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo
  • Motar, fara tas samfurin SUV gudunmawar biki ce daga wani kamfani, inda shi kuma Davido ya ga dacewar kawai ya damkawa amaryarsa a matsayin kyauta saboda murnar ranar aurensu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos- Shahararren mawaki David Adeleke da aka fi sani da Davido ya gwangwaje amaryarsa, Chioma da kyautar dalleliyar mota samfurin SUV.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun mamaye fitaccen gari a Zamfara, dan majalisa ya nemi dauki

Motoci guda biyu da kamfanin GAC motors ya ba su a matsayin kyauta na murnar ta ya su angoncewa ya dauki hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta ganin yadda ta ke da tsada kwarai.

Chioma Adeleke
Amaryar Davido ta samu kyautar mota Hoto: Chioma Adeleke
Asali: Facebook

Punch News ta wallafa cewa an bayyana motar ce fara tas bayan iyayen amarya da ango sun sanyawa aure albarka, yayin da kamfanin da ya yi kyautar motar ya taya su murnar kulla igiyar aure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Auren Davido ya tara manyan mutane

A yau ne fitaccen mawaki, Davido ya kulla igiyar aure da masoyiyarsa da su ka fara soyayya tun kafin ya shara,Chioma.

Daurin auren na su da ya hada da na gargajiya da kuma na coji ya samu halartar manya-manyan mutane, musamman daga Kudancin kasar nan.

Tashar Channels ta wallafa cewa daga hamshakan da su ka halarci taron akwai tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, tsohon gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel.

Kara karanta wannan

IPMAN: Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Arewa, an gano dalilin tashin

Sauran manyan mutane da aka hango a taron bikin akwai gwamnan jihar Edo, gwamnan Ogun da 'dan shugaban kasa Seyi Tinubu sai kuma Sanata Daisy Danjuma.

Davido ya goge bidiyon rashin da'a

A baya mun kawo labarin cewa fitaccen mawaki Davido ya goge bidiyon waka da ke nuna rashin da'a ga addinin musulunci wanda ya jawo cece-kuce tsakanin jama'a.

Daya daga cikin yaran mawakin, Logos Olori ne ya hau kan wakar, wanda tuni musulmi su ka yiwa faifan bidiyon tofin Allah tsine wanda ya kai cire shi daga shafin Davido.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.