Matar da Mijinta Ya Sake Ta, Tayi Dace da Ta Roki Alfarma Wajen Tafsir a Dawo da Ita

Matar da Mijinta Ya Sake Ta, Tayi Dace da Ta Roki Alfarma Wajen Tafsir a Dawo da Ita

  • Wata mata da ta nemi Sheikh Jabir Sani Maihula ya roki mai gidanta ya maida ta gidan ta na aure bayan ya sake ta
  • Malamin musuluncin ya shiga ya fita, ya hada wannan Bawan Allah da girman Ubangiji SWT da azumin Ramadan
  • A karshe Dr. Jabir Sani Maihula ya yi nasara, mutumin nanya dawo da igiyar aurensa da mahaifiyar ‘ya ‘yansa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Sokoto - Za a iya cewa wannan baiwar Allah ta yi dace da dare mai alfarma na lailatul kadri domin kuwa ta dawo gidan masoyinta.

Wannan mata ta ci alfarmar azumin watan Ramadan da ake yi, ta kawo kukan mahaifin ‘ya ‘yanta bayan da ya tsinka igiyar aurensu.

Kara karanta wannan

Imam Odankaru: Gwamnati ta bar tsohon malamin makaranta a kuncin rayuwa bayan ritaya

Aure Maihula
Dr. Jabir Sani Maihula ya maida aure wajen tafsirin Ramadan a Sokoto: Jabir Sani Maihula
Asali: Facebook

An kawo kukan aure wajen Jabir Maihula

Kamar yadda aka ji a bidiyo, matar nan ta rubuta takarda zuwa ga Dr. Jabir Sani Maihula, ta na neman a dawo da aurenta da sahibinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda ta shaida a takardarta, saki daya ne ya shiga tsakaninta da mai gidan wanda kullum yana halartar tafsirin babban malamin.

Da samun takardar matar, sai Dr. Jabir Sani Maihula ya shiga tsakani, ya roki tsohon mijin nata ya yi hakuri ya dawo da matarsa ta aure.

Kamar yadda Ibrahim Shehu Giwa ya fada a Facebook, an yi wannan ne a wajen tafsirin Kur’anin ranar 23 ga Ramadan a garin Sokoto.

Fitaccen malamin musuluncin ya roki mijin ya duba alfarmar Ramadan, Kur’ani da dinbin mutanen kwarai masu azumi da ke majalisinsa.

Jabir Sani Maihula ya yabi Mai gidan

Kara karanta wannan

Dala ta yi muguwar faɗuwa, ta dawo ƙasa da N700 a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

Dr. Jabir Sani Maihula ya kuma yabi halin mai gidan ganin yadda aka yi masa shaida da halartar wajen da ake fassara littafin Allah SWT.

Shehin ya yi wa mutumin shaidar fahimtar musulunci tun da ya tsaya a kan saki daya, akasin sakin bidi’a da ake yi biyu ko uku a take.

A jawabinsa, malamin wanda shi ne kwamishinan addinan Sokoto ya tunawa mutumin kaunar da uwar ‘ya ‘yarsa take yi masa har yau.

A karshe Sheikh Maihula ya maida aure

Bayan kashegari sai ga malamin ya zo da albishir wajen karatu, ya fara sanar da al’umma cewa wannan mutumi ya ji magana, ya maida ta.

Kamar yadda masu bibiyar malamin suka bayyana a Facebook, Dr. Maihula ya ja hankalin wannan mata bayan an maida gidan auren nata.

Ana zakkan kono da kudi a musulunci?

A wannan lokaci wasu suna tambaya ko za a iya bada kuɗi maimakon abinci a zakkar fidda-kai, kun ji labarin amsar Jamilu Yusuf Zarewa.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa kwararren masani ne a kan bangaren fikihu, ya amsa wannan tambaya, ya ce abin da ya fi shi ne a ba da hatsi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel