“Munafurci Ne”: Jarumar Fim Ta Caccaki Kiristoci Kan Murnan Auren Davido

“Munafurci Ne”: Jarumar Fim Ta Caccaki Kiristoci Kan Murnan Auren Davido

  • Fitacciyar jarumar fina-finai, Merit Gold Eberechi ta caccaki Kiristoci 'yan uwanta kan yadda suke murna da auren Davido duk da haihuwarsu a layi
  • Jarumar ta ce munafurci ne a rinka sukar wasu musamman mamboibn coci idan sun yi haka amma ana murna da auren Davido
  • Eberechi ta shawarci jama'a su tabbatar kafin aikata wani kuskure sun nemi kudi domin shi ne kawai zai kare su daga suka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Jarumar fina-finai, Merit Gold Eberechi ya jawo kace-nace a kafofoin sadarwa kan auren mawaki, Davido.

Eberechi ta ce Kiristoci sun nuna munafurci wurin taya mawakin murnan aurensa duk da haihuwar yara uku kafin aure.

Kara karanta wannan

Kotu ta tasa keyar 'Sanata' zuwa kurkuku saboda zargin damfarar 'yar kasar waje

Fitacciyar jarumar fim ta caccaki Kiristoci kan bikin Davido
Jarumar fim ta nuna damuwa kan yadda Kiristoci suke murnan auren Davido duk da yaran da suka haifa. Hoto: @meritgold_eberechi, @davido.
Asali: Instagram

Auren Davido: Jarumar fim ta soki Kiristoci

Jarumar ta bayyana haka ne a shafinta na Instagram a jiya Laraba 26 ga watan Yunin 2024 inda ta nuna rashin jin dadinta kan haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce Kiristoci da dama sun taya Davido da Chioma murnan bikinsu duk da sun sani sun haifi yara uku a layin banza.

"Kiristoci suna taya Davido murnan aure duk da kowa ya sani sun haifi yara uku ba ta hanyar aure ba, amma za su caccaki mambobin cocinsu kan haka."
"A rayuwa duk yadda zaka yi kawai ka nemi kudi kafin ka yi wani kuskure da mutane za su addabe ka."

- Merti Gold Eberechi

Jarumar ta shawarci jama'a su nemi kuɗi

Eberechi ta koka kan yadda ake caccakar sauran jama'a idan hakan ta faru amma idan manyan mutane ne kuma shiru za ka ji.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Ta ce ana yawan kushe mutane da ke aikata haka amma mafi yawa sai murna suke da tofa albarkacin bakinsu kan auren Davido.

Jarumar fim ta caccaki Kiristoci kan auren Davido

Davido ya ba Chioma kyautar motar alfarma

Kun ji cewa Shahararren mawaki David Adeleke da aka fi sani da Davido ya gwangwaje amaryarsa, Chioma da kyautar dalleliyar mota samfurin SUV.

Motoci guda biyu da kamfanin GAC motors ya ba su a matsayin kyauta na murnar tayasu su angoncewa ya dauki hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.