“An Yaudare Ni”: An Fasa Daura Aure Bayan Ango Ya Gano Amarya Ta Yi Ciko a Mazaunai

“An Yaudare Ni”: An Fasa Daura Aure Bayan Ango Ya Gano Amarya Ta Yi Ciko a Mazaunai

  • Wani ango ya kekashe kasa ya ce ya fasa auren masoyiyar da ya so yin rayuwa da ita saboda ya gano tana amfani da ciko a mazaunanta
  • Tsawon lokacin da masoyan suka shafe, angon bai taba ankara da cewar masoyiyar ta sa na yin ciko ba sai da aka zo yin hotunan kafin aure
  • Fitacciyar mai ayyukan jin kai, Fauziyya D. Sulaiman ta yi kira ga 'yan mata da su gyara halayensu musamman a kan yin ciko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Wasa wasa dai dabi'ar mata ta yin ciko a mazaunai ko a mamansu ta fara zama tamkar annoba a Arewacin Najeriya, yayin da a hannu daya ta zama ruwan dare.

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada sabon Amirul Hajjn jihar Kano

Fitacciyar mai ayyukan jin kai a jihar Kano, Fauziyya D. Sulaiman, ta labarta yadda wani ango ya fasa auren masoyiyarsa bayan ya gano cikon mazaunai ta yi.

Amarya ta yi ciko a mazaunai
Ango ya fasa aure saboda ya gano amarya ta yi ciko a mazaunai. Hoto: Iuliia Komarova
Asali: Getty Images

Daga bleaching mata sun koma ciko

A labarin da Hajiya Fauziyya D. Sulaiman, wacce mai taimaka wa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ce kan harkokin jin kai ta wallafa a Facebook, angon ya ce amaryar ta yaudare shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa wasu matan Hausawa sun fi gane shafa man bleaching domin canja launin fatarsu, sai dai ita ma kasuwar ciko a yanzu ta fara karbuwa a wajen matan.

Yayin da wasu ke amfani da mazaunai da maman roba ko soso, wasu kuma sun gwanance inda suka zuwa asibiti ana yi masu tiyata domin abin ya zama kamar 'haka na zo da shi.'

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

Amarya ta yi ciko a mazaunai

Bari dai mu duba labarin wadannan masoyan da auren su ya zo ƙarshe tun ba a daura ba saboda wannan matsalar ta yin ciko.

Fauziyya D Sulaiman ta ce:

"Yau na ga abin da ya ishe ni, ciko ya hana aure."

Marubuciyar fina-finai da littattafan Hausa ta ci gaba da cewa:

"Ana tsaka da yin pre-wedding pictures (hotunan kafin aure), ango ya gano mazaunan roba amaryar ta saka.
"Ai kuwa ya dire ya ce sam an yaudara shi. Yanzu dai maganar da ake yi babu wannan biki."

A karshen labarin da ta bayar, Hajiya Fauziyya ta yi kira ga 'yan mata da su gyara halayensu na son yin ciko babu gaira babu dalili.

Fasto ya gargadi mata kan yin ciko

A wani labarin, mun ruwaito cewa Fasto Daniel Olukoya ya gargadi mata masu yin irin ciko a mazaunai ko mama yana mai cewa tabbas shaidan ya riga ya yi fitsari a kansu.

Kara karanta wannan

Harin masallacin Kano ya haifar da marayu da Zawarawa da dama

Ya ce irin wadannan mata ba su gamsu da halittar da ubangiji ya musu ba kuma shaidan ba zai bata lokacinsa a kansu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel