Labaran kasashen waje
A labarin nan, za a ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ce ba za ta nade hannayenta Amurka ta shiga yakin da ake yi Isara'ila ba, za ta dauki matakan kariya.
Trump na tunanin shiga rikicin Iran-Isra'ila, ya yi barazana ga Khamenei. Sai dai Iran ta ce wannan ba yaƙin Amurka ba ne, kuma za ta ci gaba da kare kanta.
Dakarun rundunar sojin juyin juya hali na Iran sun sanar da kaddamar da hare-hare zagaye na 15 kan manyan biranen Isra'ila, sun ce za su farmaki wuraren soji.
Isra'ila ta yi barazana ga ran jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei. Ministan tsaron Isra'ila ya bayyana cewa bai kamata Khamenei ya rayu ba.
Jamhuriyar musuluncin Iran ta bayyana alamun zs ta halarci zaman tattaunawar ɓeman masalaha a yakin da ya ɓarke tsakaninta da Isra'ila, ta karɓi tayin Trump.
A labarin nan, za a ji cewa Iran ta harba makamai sassa daban-daban na Isra'ila, inda a safiyar yau ta illata wani babban asibitin tiyata da ke Kudancin kasar.
Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa Iran ta kara harbo makamai 30 masi ƙinzami amma an yi nasarar kakkaɓo masu ba tare da raunata kowaba da daddare.
Jamhuriyar musuluncu ta Iran ta gargaɗi kafatanin mutanen birnin Haifa na Isra'ila su hanzarta tattara kayansu su bar garin domin kaucewa haɗarin da ke tafe.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce babu wanda ya san ko zai shiga faɗan Isra'ila da Iran kao ba zai shiga ba, ya ce abubuwan sun canza a mako 1.
Labaran kasashen waje
Samu kari