Wata Mata Ta Fara Rasa Ganinta Tun Bayan da Ta Sauya Launin Idanunta Zuwa Shudi

Wata Mata Ta Fara Rasa Ganinta Tun Bayan da Ta Sauya Launin Idanunta Zuwa Shudi

  • Wata mata ‘yar kasar Australia da ta yiwa idonta fentin ‘tattoo’mai launin shudi ta shiga tashin hankalin rasa ganinta, tana kwance a asibiti
  • Matar mai ‘ya’ya biyar mai suna Anaya Peterson ta kwaikwayi Amber Luke, wata fitacciya ‘yar kwalliya mai shudin idanu
  • Matar mai karanta ilimin shari’a ta yi dana-sanin kin sauraran shawarin diyarta mai shekaru bakwai kacal

Australia - Wata mata mai suna Anaya Peterson ta yi dana-sanin kin bin shawari da gargadin diyarta mai shekaru bakwai da tace kada ta kuskura ta sauya launin idanunta.

An ruwaito cewa, yarinyar ta shawarci uwarta cewa, kada ta sauya launin idonta, hakan zai iya kai ta ga rasa idanun nata gaba daya.

Matar mai karanta ilimin shari’a dai ta kwaikwaiyi wata fitacciya ce, Amber Luke, wacce ‘yar kasar Australia ce da ke launin shudin idanu.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Daga Dirarriyar Budurwa Zuwa Sukurkutacciyar Matar Aure, Ta Fashe da Kuka Tare da Dora Laifi kan Mijinta

Mata ta fara makancewa saboda sauya launin idanunta
Wata Mata Ta Fara Rasa Ganinta Tun Bayan da Ta Sauya Launin Idanunta Zuwa Shudi | Hoto: nypost.com
Asali: UGC

Ita kanta Luke ta sauya launin idanunta ne a shekarar 2019, kuma ta sha fama da makantan wucin gadi na tsawon makwanni uku lokacin da aka yi mata aikin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Daily Mail ta ce, matar mai ‘ya’ya biyar a yanzu haka tana asibiti tun bayan da aka yi mata aikin sauya launin idanu zuwa shudi, domin tana rasa ganinta.

Akwai yiwuwar Anaya ta rasa ganinta

Jaridar ta ce, akwai yiwuwar matar mai shekaru 32 ta rasa ganinta gaba daya duba da yanayin da ta tsinci kanta da kuma tasirin tawadar da aka yi amfani da ita wajen sauya launin idanun.

A baya can, an yiwa Anaya aikin raba harshenta gida biyu tare da yin zane-zane masu yawa a fuska, amma a yanzu ta yanke shawarin sauya idanunta a matsayin sawani sabon salo.

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwar da ‘Dan Uwanta Ya Hakura da Karatu don Ta Kammala Nata ya Taba Zuciya, Ta Nuna Masa Tsabar Ladabi

Duk da fuskantar matsanancin ciwon kai da bushewar idanu a matsayin somin waraka, ta yanke shawarin a sake yi ma kanta aikin idon hagu a Disamban 2020.

Bayan watanni ba tare da wata matsala ba, Anaya ta wayi gari wata rana a watan Agustan 2021, inda taga idanunta sun kumbura suntum.

Diyarta ta gargade ta game da aikin sauya launin idanu

Anaya ta bayyana cewa, a tun farko diyarta ta gargade ta game da wannan aikin mai hadari, inda tace yarinyar ta ji tsoron kada ta rasa idanunta gaba daya, CornWallLive ta tattaro.

A yanzu dai Anaya na fuskantar rasa gani, domin idanunta sun fara makancewa a hankali, lamarin da ya tada hankalinta.

A cewarta:

“Da fari na yiwa ido daya ne saboda a tunani na ko da na makanci, akalla ina da sauran ido daya.
“Ya kamata na tsaya haka ne. Diyata ta gargade ni kada na sake yi, tace idan na makance fa? Ita dai bata yarda da hakan ba.”

Kara karanta wannan

Dole Ta Yi Masa? Ango Ya Yi Jugum Yana Kallon Amaryarsa Yayin da Take Girgijewa Ita Kadai A Bidiyo

Dan Adam ya cika ganganci da abin da ya yi yakini a kai, haka wani matashi ya sheke dan uwansa garin gwada maganin bindigan da aka bashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel