Haramta Shan Barasa a Qatar Na Taimakawa Mata Su Yi Kallon Kwallo Cikin Aminci

Haramta Shan Barasa a Qatar Na Taimakawa Mata Su Yi Kallon Kwallo Cikin Aminci

  • Wata mai kallon kwallon kafa kuma fitacciyar ‘yar gwagwarmaya ta bayyana abin da ta gani a kasar Qatar
  • Ellie, ‘yar kasar Ingila ta ce dokokin da aka sa a Qatar sun taimaka wajen dakile faruwar barna sosai kan mata
  • Ta ce ta samu natsuwar kallon kwallo fiye da yadda take kallo a kasar Ingila, inda ake hantarar mata

Qatar - Wasan da ake bugawa na gazar cin kofin duniya a kasar Qatar ya jawo cece-kuce tun bayan haramta wasu abubuwa da dama na rashin da’a

Sai dai, hakan ya sa maza sun yi karatun ta natsu tare da koyar da darasi ga masu hantarar mata a filayen kwallon kafa a sauran kasashen duniya.

Ellie Molloson, ‘yar shekaru 18 mai goyon bayan kulob din Nottingham Forest kuma ‘yar fafutukar samar da aminci ga mata a filin kwallo ta ce da fari ta ji tsoron zuwa kasar domin goyon bayan Ingila a gasar ‘World Cup’ ta bana.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya ce man fetur ba zai iya rike Najeriya, ya fadi mafita ga tattalin arziki

Sai dai, a cewarta, ta ga sabanin haka, domin bata taba tsammanin samun natsuwa da kwanciyar hankali gami da rashin hantara daga maza ba a filin kwallon.

Mata sun bayyana abin da suka gani a Qatar
Haramta Shan Baraza a Qatar Na Taimakawa Mata Su Yi Kallon Kwallo Cikin Aminci | Hoto: thetimes.co.uk
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta shaidawa a iTv cewa:

“Ban yi tunanin zan kasance cikin aminci ba a nan. Da fari a dame nake ko idan na nuna fata ta za a kama ni...sai dai ba haka lamarin yake ba ko kada. Na ji matukar nautsawa da aminci”
“Ban samu wata kira ta batsa ba ko martani mara dadi ba da watakila zan iya samu a Ingila ba.
“Sun kasance masu matukar karbar baki da karimci.”

Kallon kwallon kafa a Qatar ya fi a Ingila tsaro ga mata

Ms Molloson dai ke jagorantar wani gangamin nemawa mata ‘yanci a filin wasan kwallon kafa da takin HerGameToo domin gangamin wayar da jama’a kan hantarar mata a filayen kwallon kafa.

Kara karanta wannan

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a jihar Delta, inda da dama suka jikkata

Ta tafi kasar Qatar ne tare da mahaifinsa da kuma mai kula da lamurranta, inda ta bayyana cewa, kallon kwallon kafa ga mata a Qatar ya fi kallonsa a Ingila.

Shi kansa mahaifinta da ya zo kasar domin ba ta kariya cewa ya yi:

“Na fito ne musamman domin na kula da ita Ellie amma maganar gaskiya yanzu babu bukatar na nuna wata damuwa."

Kwallon kafa na daya daga abubuwan da ke da muhimmanci a nahiyar Turai, musamman kasar Ingila, an dauko batutuwa da suka shafi shan barasa a filiyen kwallo, rahoton Financial Times.

Masu kallo da dama suna da yakinin cewa, haramta shan giya ne ya jawo wasannin ke tafiya daidai ba tare da hantarar mata ba.

A tun farko kun ji cewa, gwamnatin Qatar ta haramta shan giya, zina da sauran manyan laifuka da aka saba yi kuma suka saba da addinin Islama a wasu kasashen turai yayin wasannin kwallon kafa.

Kara karanta wannan

Subut da baka: Tinubu ya sake yin wata katobarar da ta fi ta baya, 'yan Najeriya sun girgiza

Asali: Legit.ng

Online view pixel