Labaran kasashen waje
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa sun san inda jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Khamenei, yake boye. Ya ce ba za a kashe shi ba.
Bayan nazarin abin da ke faruwa a rikicin Iran da Isra'ila, akwai bukatar mu kalli tasirin rikicin kasashen ga tattalin arzikin duniya, musamman farashin mai.
Gidan talabijin na Iran ya sanar da kai hare-hare karo na 10 a jerin farmakin ramuwar gayya da kasar ke kai wa kan Isra'ila bayan ɓarkewar rikici tsakaninsu.
Rasha ta kai hari mai tsanani kan Kyiv, inda ta kashe mutane 15. Shugaba Zelenskyy ya kira harin da mafi muni yayin da ya nemi kasashen duniya su ce wani abu.
Hukumomin da ke kula da harkokin sufurin jiragen sama a Indonesia sun canza wa wani jirgin alhazai wurin sauka bayan samun saƙon barazanar bam a ciki.
Tankokin yakin Isra'ila sun bude wuta kan Falasdinawan da suka je wurin karbar abinci a zirin Gaza. An samu asarar rayuka sakamakon wutar da sojoji suka bude.
Tehran ta fara zama kufai yayin da mazauna birnin ke ƙoƙarin tserewa saboda fargabar hare-hare. Isra'ila ta ce ta kai hare-hare masu yawa kan biranen Iran.
Mutane sama da 300,000 sun bar gidajensu bayan harin bama-baman da Isra'ila ta ƙara kaiwa birnin Tehran yayin da Iran ta nuna alamun amincewa da batun sulhu.
Isra'ila ta kashe sabon babban hafsan sojojin Iran, Ali Shadmani, a harin da ta kai Tehran. An ji fashe-fashe biyu a Tabriz, yayin da rikicin ya shiga kwana na 5.
Labaran kasashen waje
Samu kari