Alkalin Amurka Ya Yi Watsi da Karar da Aka Shigar Kan Yariman Saudiyya Bisa Kisan Khashoggi

Alkalin Amurka Ya Yi Watsi da Karar da Aka Shigar Kan Yariman Saudiyya Bisa Kisan Khashoggi

  • Kasar Amurka ta bayyana bukatar janye karar da aka shigar kan yariman Saudiyya, Muhammad bin Salman
  • A 2018, an zargi yariman da kashe wani fitaccen dan jarida kuma dan gwagwarmaya a kasar Turkiyya
  • Alakar siyasa da batutuwan da suka shafi diflomasiyya ne yasa aka yi watsi da batun gurfanar da yariman a Amurka

Amurka - A ranar Talata ne wani alkali a kasar Amurka ya yi watsi da karar da aka shigar kan yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman bisa zargin hannu a kisan dan jarida Jamal Khashoggi a 2018.

Mai shari’a John Bates ya karbi takardar matsaya daga gwamnatin Amurka mai cewa, yarima Salman wanda a yanzu shine firayinminista a Saudiyya na da kariyar shugabanci, don haka ba za a iya gurfanar dashi a kotun kasar ba, Channel Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Bayyana Asarar Naira Tiriliyan 10 da ke Jiran Najeriya a 2023

Mata=sayar Amurka kan yiwuwar daure Muhammad bn Salma
Alkalin Amurka Ya Yi Watsi da Karar da Aka Shigar Kan Yariman Saudiyya Bisa Kisan Khashoggi | Hoto: vox.com
Asali: UGC

Bates ya ce, karar da matar Khashoggi Hatice Cengiz da kungiyar gwagwarmayarsa ta DAWN suka shigar ta yi bayanai da martani mai daukar hankali, inda suka bayyana yiwuwar hannun yariman a kisan na 2018.

Amma da yake hukunci, Bates ya ce bai da ikon kin bin umarnin matsayar gwamnatin Amurka da ya samu a cikin wata takarda da aka kawo gabansa a ranar 17 ga watan Nuwamba, wacce ta bukaci yin watsi da karar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nada yariman na da alaka da batun watsi da karar?

Duk da cewa makwanni kadan da suka gabata ne aka nada yariman a matsayin firayinminista, kasar Amurka da Saudiyya tun a baya na da kwance na diflomasiyya, kuma kokarin hukunta Salman a kotun kasar zai iya shafar alakar kasashen biyu.

A cewar alkalin, hujjojin zargin kisan Khashoggi, nada yariman a matsayin firayinminsta da kuma matsayar Amurka a kan batun karar sun ba shi wahala sosai.

Kara karanta wannan

Kada Kuji Tsoron Za'ai Fari Ko Karancin Abinci, Mun Tanadi Filayen Noma - NALDA

Don haka yace, ba shi da wani zabin da ya wuce a jiye batun karar gaba dayanta.

Alakar Yarima bn Salman da Kashoggi

Yarima Salman ya kasance shugaba a kasar Saudiyya da ke rabar inuwar mahaifinsa na tsawon shekaru.

Daya daga cikin masu sukar yariman, Khashoggi wani dan jarida ne kuma dan gwagwarmaya mazaunin Amurka.

Khashoggi ya rasa ransa ne a lokacin da ya tafi kasar Turkiyya tare da budurwarsa domin karbar takardun aure a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul.

Bayan shigansa ofishin jakadancin, a nan aka kashe shi tare da narkar da gawarsa, lamarin da ya jawo cece-kuce da tsamin zama tsakanin Amurka da Saudiyya.

An sha zargin Salman da wannan kisa, wannan yasa ake ta cece-kuce da sukar yariman a fadin duniya.

A 2020, kasar Saudiyya ta tasa keyar wasu mutum bakwai zuwa magarkama na tsawon shekaru 20 bisa zarginsu da wannan kisa.

Idan baku manta ba, a 2019 ya bayyana cewa, kisan Jamal Kashoggi ya rataya a wuyansa, kamar yadda rahotanni suka fada.

Kara karanta wannan

Nagode Mama: Aminu Adamu ya Bada Hakuri a Fili, Yayi Alkwari Zai Gyara Halinsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.