Mawaki Davido Zai Jagoranci Wasannin Bikin Rufe Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar

Mawaki Davido Zai Jagoranci Wasannin Bikin Rufe Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar

  • Yayin da ake gab da batun rufe wasan cin kofin duniya, Davido ne zai jagoranci wasannin da za a yi a ranar rufewar
  • An gayyaci Davido a tun farko, amma aka samu akasi dansa mai shekaru uku ya rasu a cikin ramin wanka a gidansa
  • An buga wasannin cin kofin duniya, inda kasashe da dama suka hallara, an cire wasu, wasu kuma sun haura zuwa wasan karshe

Fitaccen mawakin nan na Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido ne zai cancara wasa a bikin rufe wasan cin kofin duniya da ake bugawa a yanzu haka a kasar Qatar.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka yi bikin bude wasannin na cin kofin duniya da karatun Al-Qur'ani da wasu wasanni masu kayatarwa.

Rahoton BBC ya bayyana cewa, Davido ne zai jagoranci wasanni da wakar taken kammala wasannin a ranar 18 ga watan Disamba.

Davido zai jagoranci bikin rufe wasan World Cup
Mawaki Davido Zai Jagoranci Wasannin Bikin Rufe Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

An kuma bayyana cewa, zai yi hakan ne tare da wasu jiga-jigan fitattu. Tribidad Cardona da Aisha ranar da za a rufe wasannin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An so Davido ya jagoranci bikin bude gasar cin kofin duniya

Davido mai shekaru 30 ya yi fice a duniyar waka, kuma an gayyace shi ne a karo na biyu kenan byana gayyatar farko da bai samu zuwa ba.

A baya an tsara cewa, Davido ne zai bude taro na wasannin cin kofin duniya, amma aka samu akasi dansa ya rasu a lokacin, Punch ta ruwaito.

Davido dai bai samu damar nishadantar da jama'a ba a wancan lokacin kasancewar dansa, Ifeanyi ya rasu kuma a lokacin yana tsaka da jimami.

A cewar rahoto, ziyarar ta kasar ce za ta zama wasa na farko da Davido zai yi tun bayan mutuwar dan nasa mai shekaru uku da ya fada a ramin wanka.

Qatar ta ce za ta daure masu zina da neman maza yayin wasannin cin kofin duniya

Qatar ta gargadi masu zuwa kallon wasanni da masu bugawa kan yin zinace-zinace da neman maza a kasar yayin wasanni.

Hakazalika, kasar ta haramta shan giya, inda tace ita kasa ce ta muslunci don haka bata amince da wannan dabi'a ba.

Wannan lamari dai ya haifar da cece-kuce a fadin duniya, inda mutane da dama ke kallon hakan a matsayin take hakkin jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel