Babban kotun tarayya
Alkalan alkalai na Najeriya, mai shari'a Olukayode Ariwoola, ya rantsar da sabbin alkalan Kotun Koli. Ariwoola ya ba su shawara kan gudanar da aikinsu.
Yayin da aka fara sauraran shari’ar zaben gwamnan jihar Kogi, kotu ta soke karar jam’iyyar APP da ke kalubalantar zaben Gwamna Ododo na jam'iyyar APC.
Rahotanni sun kawo cewa Kotun Musulunci ta aike da Ramlat Mohammed zuwa gidan gyaran hali saboda zargin ta da koyar da karuwanci da kuma yada badala.
Hukumar ICPC ta gurfanar da Bola Audu, tsohon babban ma’aikaci a ofishin Akanta Janar na tarayyar Najeriya, bisa zargin karkatar da naira miliyan 72.
Alkalin kotun Musulunci da ke zama a yankin Kumbotso ta jihar Kano, Mai Shari’a Nura Yusuf Ahmed, yankewa matashin da aka kama da Murja Kunya daurin watanni 6.
Yayin da ake zargin akwai cin hanci da rashawa a bangaren shari'a, da alamu akwai kamshin gaskiya bayan shugabar alkalan jihar Neja ta tabbatar da haka.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta haramtawa Gwamna Abba Kabir rusa wasu gidaje a Unguwar Salanta bayan an shirya rushe su a yankin.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ci gaba da tuhumar Burgediya-janar na soja kan zargin badakalar kudade.
A yau ake jin Hukumar EFCC tayi nasara, kotu ta yankewa Mama Boko Haram da wasu hukuncin dauri. A. I Arogha shi ne lauyan da ya tsayawa EFCC a shari’ar.
Babban kotun tarayya
Samu kari