Bidiyo: Wata Mata Ta Shiga Babbar Matsala Bayan Ta Ci Zarafin Jami'ar 'Yar Sanda a Legas

Bidiyo: Wata Mata Ta Shiga Babbar Matsala Bayan Ta Ci Zarafin Jami'ar 'Yar Sanda a Legas

  • An aike da wata mata zuwa gidan gyaran hali na Kirikiri bisa zarginta da cin zarafin wata ƴar sanda a yankin Ajah da ke jihar Legas
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu cikin wata sanarwa
  • Hundeyin ya yi ƙarin bayani kan lamarin inda ya sanya wani faifan bidiyo da ya nuna ƙarara abin da matar ta yi wa jami’ar wacce ke sanye da kayan aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta gurfanar da Omorogbe Jennifer Soni, ƴar shekara 26 da haihuwa, wacce aka gani a cikin wani faifan bidiyo tana cin zarafin wata ƴar sanda a Ajah, Legas, a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu, 2024.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta yi kamu mafi girma a tarihinta, bayanai sun fito

Kamar yadda bidiyon ya nuna Omorogbe ta yi zazzafar gardama da jami’ar ƴar sandan, kuma a lokacin da ta yi yunƙurin zuwa kusa da motarta, Omorogbe ta ture jami’ar, lamarin da ya sa ta faɗi ƙasa.

Kotu ta tura wata mata gidan gyaran hali
Matar ta tsinci kanta a gidan gyaran hali kan abin da ta aikata Hoto: @BenHundeyin
Asali: Facebook

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka tura matar zuwa gidan gyaran hali?

Hundeyin ya bayyana cewa tsare ta ya biyo bayan gurfanar da ita ne a gaban kotu bayan da aka ɗauke ta a bidiyo tana cin zarafin jami'ar.

An gurfanar da matar a kotun majistare ta Etiosa, Ajah, kuma an tsare ta a gidan gyaran hali na mata na Kirikiri har zuwa zamanta na gaba a ranar Laraba, 27 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Yan sanda da sojoji sun yi kazamin artabu da ƴan bindiga, sun samu nasara a jihar Arewa

Ya rubuta cewa:

“An gurfanar da Omorogbe a gaban kotu a washegarin ranar 22 ga watan Fabrairu, 2024 a kotun majistare ta Etiosa, Ajah, kuma an tasa ƙeyar ta zuwa gidan gyaran hali na mata a Kirikiri har zuwa ranar 27 ga watan Maris, 2024.
"Rundunar ƴan sandan jihar Legas na shawartar mazauna Legas da su kasance masu bin doka da oda a harkokinsu na yau da kullum tare da kowa da kowa domin duk wanda aka samu da laifin karya doka za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Ƴan Sanda Sun Gwangwaje Masu Zanga-Zanga a Legas

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya a Legas sun raba masu zanga-zanga ruwan roba da biskit.

Masu zanga-zangar dai sun fito kan titina ne domin nuna rashin gamsuwa kan halin yunwa da tsadar rayuwa da ake fama da su a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel