Kakakin Majalisar PDP a Arewa Ya Shiga Matsala Bayan APC Ta Masa Barazana Kan Wani Dalili

Kakakin Majalisar PDP a Arewa Ya Shiga Matsala Bayan APC Ta Masa Barazana Kan Wani Dalili

  • Jam'iyyar APC ta yi barazanar maka kakakin Majalisar jihar Plateau a kotu kan kin rantsar da mambobinta
  • Jam'iyyar ta ce za ta dauki mataki kan kakakin Majalisar, Hon. Gabriel Dewan kan biris da rantsarwar da 'yan Majalisu 16
  • Wannan na zuwa ne bayan Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben mambobin PDP tare da bai wa mambobin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Jamiyyar APC a jihar Plateau ta yi barazanar zuwa kotu kan kakakin Majalisar jihar saboda kin rantsar da mambobin Majalisar.

Jam'iyyar ta ce za ta dauki mataki kan kakakin Majalisar, Hon. Gabriel Dewan kan biris da rantsarwar da 'yan Majalisu 16 a Majalisar.

Kara karanta wannan

Kamfanin Ajaokuta: Majalisa za ta binciki gwamnatin Yar'adua, Jonathan da Buhari kan fitar da $496m

Jam'iyyar APC ta yi barazana ga kakakin Majalisa kan wani laifi
APC ta ce lokaci suke jira idan bai yi abin da ya dace ba. Hoto: Hon. Gabriel Dewan, Umar Ganduje, Caleb Mutfwang.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene matakin da APC ke son dauka?

'Yan majalisun 16 sun samu nasara ne bayan Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben mambobin jam'iyyar PDP, cewar Tribune.

Idan ba manta ba, a ranar Litinin 26 ga watan Faburairu kotu ta yi fatali da korafin jam'iyyar PDP inda suke kalubalantar hukuncin kotun.

Mambobin jam'iyyar PDP su na kalubalantar hukuncin ne bayan Kotun Koli ta tabbatar da zaben Gwamna Caleb wanda suke jam'iyya daya.

Shugaban jam'iyyar APC, Hon. Rufus Bature ya nuna damuwa kan matakin na kakakin Majalisar inda ya ce ya raina hukuncin kotu ne.

Martanin jam'iyyar APC kan lamarin

Bature ya bukaci Dewan ya yi gaggawar rantsar da mambobin ko ya fuskanci shari'a, cewar Daily Trust.

A cewarsa:

"Ba za mu tilasta Dewan rantsar da mambobin ba, za mu ba shi lokaci mu gani ko zai yi hakan.

Kara karanta wannan

Yayin da ake samun matsala a aure kan wasu dalilai a Kano, Majalisa ta dauki mataki don dakile haka

"Tabbas za mu yi wani abu a kai, akwai hanyoyin shari'ar da za mu bi idan hakan ya zama dole.
"Ya kamata tun farko ace ya yi hakan, mutanen da suke ƙirƙirar doka amma su ne ke jawo cikas basu son bin doka."

Gwamna Caleb ya dawo da ma'aikata aikinsu

Kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Mutfwang Caleb ya yi abin a yaba bayan dawo da ma'aikata bakin aiki.

Ma'aikatan an dakatar da su ne saboda yadda gwamnatin baya ta dauke su ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel