Tabbas Akwai, Shugabar Alkalai a Jihar Arewa Ta Fasa Kwai Kan Zargin Cin Hanci a Bangaren Shari'a

Tabbas Akwai, Shugabar Alkalai a Jihar Arewa Ta Fasa Kwai Kan Zargin Cin Hanci a Bangaren Shari'a

  • Yayin da ake zargin cin Hanci da rashawa a bangaren Shari'a, shugabar alkalan jihar Neja ta yi magana a kai
  • Mai Shari'a, Halima Ibrahim wacce ita ce shugabar alkalan jihar Neja ta ce tabbas akwai cin hanci da rashawa a bangaren
  • Halima ta ce korafe-korafen da ake a wasu bangare cewa akwai rashawa bangaren ba za a kawar da hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Neja - Zarge-zargen da ake yi cewa akwai cin hanci da rashawa a bangaren Shari'a, da alamu akwai kamshin gaskiya.

Shugabar alkalan jihar Neja, Mai Shari'a, Halima Ibrahim Abdulmmlik ta tabbatar da haka yayin wani taro a jihar, cewar Arise TV.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka kama masu laifi 400 a jihar APC

Zargin cin hanci da rashawa a bangaren Shari'a y fara zama Gaskiya
Shugabar Alkalai a Neja Ta Magantu Kan Zargin Cin Hanci a Bangaren Shari'a. Hoto: Olukayode Ariwoola.
Asali: Twitter

Mene Halima ke cewa kan cin hanci?

Mai Shari'a, Halima ta ce korafe-korafen da ake a wasu bangare cewa akwai rashawa bangaren Shari'a ba za a iya kawar da hakan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabar alkalan ta bayyana haka ne a yayin taron mako na kungiyar Lauyoyin Najeriya, NBA reshen jihar da aka gudanar a birnin Minna.

A cewarta:

"Tabbas akwai cin hanci kamar yadda wasu ke zargi ko da a zahiri ne ko kuma hasashe.
"Ya kamata a bangaren Shari'a a dakile duk wani nauyi na cin hanci don wanke bangaren daga zarge-zargen.
"Kamar yadda muka sani cin hanci ba wai karbar kudade ba ne ta hanyar da bai dace ba, hatta yadda lauyoyi ba sa bin shari'ar wadanda suke karewa da gaskiya shi ma cin hanci ne."

Ta shawarci lauyoyi da su tabbatar sun bi tsarin aikinsu kamar yadda suka koya wurin gudanar da ayyukansu, kamar yadda Thisday ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: An bukaci Shugaba Tinubu ya gaggauta yin murabus, karin bayani ya bayyana

Wannan na zuwa ne bayan Sanata Elisha Abbo ya zargi cewa cin hanci a bangaren shari'a ya zama ruwan dare.

Kotu ta dakatar da EFCC kan tuhumar soja

A baya, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da dakatar da hukumar EFCC kan ci gaba da tuhumar wani Burgediya-janar a Najeriya.

Ana zargin Burgediya-janar Nengite Charles ne da karkatar da makudan kudade lokacin da ya ke kula da hukumar NDDC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel