Yan bindiga
A garin Dyom, da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benue, wasu makiyaya dauke da makamai da ‘yan bindiga sun mamaye gonaki da gidaje a yankin. Sun hana mutane fita.
Jami’an tsaro a jihar Imo sun cafke wasu manyan ‘yan ta’adda biyu tare da masu daukar nauyinsu, inda aka kwato bindigogi, harsasai da masu tsafi.
Jiragen yakin rundunar sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga a jihar Neja. Farmakin ya jawo an hallaka 'yan bindiga masu yawan gaske.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun tara shanun sata sama da 200, suka sako su cikin gonaki a karamar hukumar Kankia da ke jihar Katsina.
Gwamnatin jihar Kebbi ta yi tsokaci kan rahotannin da ke cewa ta nemo sojojin haya daga kasashen waje domin taimaka mata yaki da 'yan bindiga da sauran miyagu.
‘Yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yan sanda a garin Zonkwa, da ke Kaduna, sun kashe jami’ai biyu; an ce sun kai farmaki ne don ‘yantar da wasu da aka kulle.
Rikici tsakanin masu hakar ma’adanai da ‘yan bindiga a Birnin Gwari, ya yi sanadin mutuwar mutane 7, yayin da mazauna suka bukaci gwamnati ta dauki mataki.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bukaci a mayar da dazuzzuka zuwa manyan gonakin noma domin magance matsalar rashin tsaro da 'yan ta'adda.
Rahotannin da ke riskarmu sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kai farmaki da safe a ƙauyen Maradawa da ke cikin yankin Rijiya, Gusau, jihar Zamfara a masallaci.
Yan bindiga
Samu kari