Yan bindiga
Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun kashe mutum hudu da suka je siyayya a babban kantin siyar da kaya na Wisfom da ke a Nasarawa.
Gwamnonin Arewa ta Tsakiya sun kai ziyarar ta'aziyya a jihar Plateau kan mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren da yan ta'adda suka kai a jihar.
An samu asarar rayuka masu yawa daga bangaren yan banga da yan bindiga a wani kazamin artabu da ya auku a tsakanin bangarorin biyu a jihar Kaduna.
Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Garam da ke jihar Neja inda suka yi garkuwa da mutum uku. Wannan shi ne karo na biyu da suke kai hari garin.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da mutane uku bayan harbe wani dan banga a Barangoni da ke Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
An yi garkuwa da Safiyanu Isa Andaha tare da wani Alhaji Adamu a yammacin ranar 1 ga Janairu, 2024 a hanyar Akwanga-Andaha. Jami'an tsaro sun bazama nemansu.
Gwamna Caleb Mutfwang, ya sanar da zaman makoki na mako guda domin girmama wadanda aka kashe a harin kananan hukumomin Bokkos, Mangu, da Barkin-Ladi.
Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai hari a jihar Plateau, ana tsaka da jimamin kisan mutum 190 da yan bindiga suka yi a kananan hukumomi biyu na jihar.
Rundunar ƴan sandan jihar Kogi ta sanar da cewa jani'anta sun samu nasarar ceto wasu mutum sama da 20 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar.
Yan bindiga
Samu kari