Yan bindiga
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ziyarci wasu kananan hukumomin Kano da ke fama da barazanar 'yan bindiga. Ya gana da jami'an tsaro da jama'ar yankunan.
Yan sandan babban binrin tarayya sun kashe ’yan bindiga uku, sun kama babban dan ta'adda, kuma sun dakile mugun shirin garkuwa da mutane a Abuja.
Gwamnatin Abia ta karyata labarin da ake yadawa cewa Gwamna Alex Otti ya sha da kyar a harin yan bindiga, ta ce wadanda aka farmaki ba ayarin Gwamna ba ne.
Dakarun Najeriya sun bayyana nasarorin da suka samu sun kashe 'yan ta'adda takwas da kama 51 tare da kama makamai a farmakin da suka kai cikin kwana uku.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da manoman da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Kaduna. Sun tafi da su zuwa cikin daji.
Mai taimakawa shugaban kasa game da harkokin tsaro ya ce Najeriya na samun tallafi daga Amurka, Faransa, Birtaniya da wasu kasashe a yaki da ta'addanci.
Ministan tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus daga mukaminsa bisa dalilan lafiya, kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da hakan.
Sarki Ojibara na Bayagan da wasu mutane shida sun tsere daga hannun ‘yan bindiga bayan artabun da jami’an sa-kai suka yi da miyagun a wani dajin Kwara.
Gwamnonin jihohin Arewa sun gudanar da taro kan matsalar rashin tsaro. Sun samo hanyoyin da suke son abi domin kawo karshen matsalar da ta addabi yankin.
Yan bindiga
Samu kari