Bayan halaka jami'an tsaro 37 a wuri daya, Gwamna ya dakatar da hakar ma'adanai a jiharsa

Bayan halaka jami'an tsaro 37 a wuri daya, Gwamna ya dakatar da hakar ma'adanai a jiharsa

  • Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Niger ya haramta hakar ma'adanai a dukkan wuraren hakarsu dake fadin jihar
  • Hakan ya biyo bayan halaka jami'an tsaro 37 da 'yan bindiga suka yi tare da sace wasu a wurin hakar ma'adanai a Shiroro
  • Gwamnan ya bukaci jami'an tsaro da su rubuto masa bayanan dukkan wuraren hakar ma'adanan jihar baki daya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Niger - Gwamnatin jihar Niger a ranar Litinin ta dakatar da hakar dukkan ma'adanai a fadin jihar kuma ta umarci hukumomin tsaro da su rubuto mata bayanai kan dukkan wuraren hakar ma'adanai da 'yan bindiga suke kai farmaki.

Wannan haramcin ya biyo bayan farmakin da 'yan bindiga suka kai wurin hakar ma'adanai dake karamar hukumar Shiroro ta jihar. A kalla mutane 45 da suka hada da jami'an tsaro 37 ne suka rasa rayukansu. 'Yan bindigan sun sace ma'aikata 'yan China har hudu tare da wasu farar hula.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan daba sun kai wa 'yan majalisa hari, sun raunata mutum 6, sun ragargaza motoci

Gwamna Abubakar Sani Bello na Niger
Bayan halaka jami'an tsaro 37 a wuri daya, Gwamna ya dakatar da hakar ma'adanai a jiharsa. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Premium Times ta ruwaito cewa, Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Matane, a wata takarda, yace hukuncin dakatar da hakar ma'adanai a jihar ya zama dole sakamakon karuwar rashin tsaro a 'yan kwanakin nan.

"Bayan farmakin 'yan bindiga a wurin hakar ma'adanai dake kauyen Ajata Aboki na karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger, Gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi umarnin dakatar da hakar dukkan ma'adanai a kananan hukumomin Shiroro, Munya da Rafi saboda farmakin da ake cigaba da kaiwa," Matane yace.

Yace dakatarwan babu ranar sassautawa, har sai baba ta gani.

"An gano cewa wadannan wuraren hakar ma'adanan su je janyo hankali tare da bai wa 'yan ta'adda mafaka wanda hakan kalubale ne ga rayuka da kadarori.
"SSG ya ja kunne cewa duk wasu masu hakar ma'adanai da aka kama a yankunan da aka lissafa zasu fuskanci fushin hukuma.

Kara karanta wannan

Na sadaukarwa da Najeriya rayuwata: Sojan da ya rasu a farmakin Shiroro

"Gwamnatin jihar ta umarci jami'an tsaro na jihar da su mayar da cikakken bayani kan dukkan wurin hakar ma'adanai a kananan hukumomin da lamarin ya shafa.
"Gwamnatin ba za ta hakura da matsalolin 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane, masu satar shanu da sauran masu kaifuka a jihar ba har sai ta kakkabo su," Matane yace a takardar.

Yayi kira ga jama'a da su bude idanuwansu tare da kai rahoton duk wani abu ko mutum da suke zargi, zirga-zirga ko wasu abubuwa a yankunan su ga jami'an tsaro.

'Yan bindiga sun sake sace wani babban fasto a Kaduna

A wani labari na daban, 'yan ta'adda a sa'o'in farko na ranar Litinin sun sake yin garkuwa da wani limamin cocin katolika, Rabaren Fada Emmanuel Silas a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Shugaban Catholic Diocese ta Kafanchan, Rabaren Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da hakan a wata takardar da ya bai wa manema labarai a Kaduna, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 17, sun sace 'yan China 4 a wurin hakar ma'adanai

Asali: Legit.ng

Online view pixel