Jihar Enugu
Sanata Chukwuka Utazi tsohon sanatan Enugu ta Arewa ya miƙa wasiƙar yin murabus ɗinsa daga zama mamba a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Kungiyar rajin kafa kasar Biafra ta kalubalanci Shugaba Tinubu da ya bayyana a kotu kan hukuncin da kotu ta yanke na ayyana kungiyar a matsayin 'yan ta'adda.
Wani sabon rahoto da aka fitar ya fayyace gaskiya kan batun sakin shugaban shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Rahoton ya nuna cewa batun ba gaskiya ba ne.
Wasu lauyoyi sun bai wa hamata iska bayan sun doku tare da fadan bakaken maganganu ga juna a cikin kotun majistare da ke jihar Enugu yayin zaman kotu.
Jam'iyyar PDP ra rasa kujerar mamban majalisar dokokin jihar Enugu mai wakiltar mazaɓar Nkanu ta gabas, Kotu ta umarci INEC ta shirya sabon zabe a wasu rumfuna.
Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamna ta yi fatali da ƙorafin ɗan takarar jam'iyyar PRP cewa takardar NYSC ta gwamna Peter Mbah jabu ce, ta ce babu hujja.
Ƴan bindiga sun tare hanya sun yi awon gaba da limamin cocin Katolika ta Enugu, Rev. Fr. M. Okide, tare da wasu mutum shida da ba su ji ba, ba su gani ba.
Kotun koli da ake wa laƙabi da Kotun daga ke sai Allah ya isa ta kori ƙarar da jam'iyyar APC ta shigar tana kalubalantar nasarar gwamna Mbah na jihar Enugu.
Kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokoki ta jiha da ke zama a Enugu ta tsige Bright Ngene na jam’iyyar Labour Party sannan ta yi umurnin sake sabon zabe.
Jihar Enugu
Samu kari