Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Zaben Gwamnan PDP, Ta Bayyana Mai Nasara

Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Zaben Gwamnan PDP, Ta Bayyana Mai Nasara

  • Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Enugu da ake yi a jihar Legas
  • Kotun yayin hukuncinta, ta tabbatar da nasarar Gwamna Peter Mbah na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe
  • Har ila yau, koyun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar LP a jihar, Edoega Jonathan da ke kalubalantar zaben

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu a jam'iyyar PDP.

Kotun ta yanke hukuncin shari'ar zaben ne a yau Juma'a 10 ga watan Nuwamba a jihar Legas.

Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamna a Enugu
Kotun ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamna. Hoto: Peter Mbah.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Enugu?

Kara karanta wannan

Murna yayin da kotun daukaka kara ta mayar da dan Majalisar PDP a jihar Arewa kujerarshi, ya gode

Har ila yau kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar LP, Edeoga Jonathan da ke kalubalantar zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit ta tattaro cewa yayin yanke hukuncin, kotun ta amince da yin duba zuwa ga dukkan matsaloli uku na dan jam'iyyar LP, Edeoga a jihar.

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a, Tani Yusuf Hassan ya yi watsi da korafin dan takarar LP inda ya ce babu hujjoji gamsassu.

Mene Alkalin kotun ya ce kan zaben?

Alkalin ya kara da cewa mai karar ya gaza kawo hujjoji musamman da za su kare korafinsa kan takardar bautar kasa ta Mbah, cewar Thisday.

Idan ba a mantaba, hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta ayyana Peter Mbah na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

Mbah ya samu kuri'u 160,895 yayin da takwaransa na jam'iyyar LP, Edoeoga na zamo na biyu da kuri'u 155,553 a zaben da aka gudanar a watan Maris.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta gama aiki, ta yanke hukunci kan nasarar dan majalisar tarayya na PDP

Kotun zabe ta tabbatar da Kingibe sanatar Abuja

A wani labarin, kotun daukaka kara ta tabbatar da Sanata Ireti Kingibe a matsayin wacce ta lashe zabe.

Kingibe wacce yar jam'iyyar LP ce ta yi nasara kan Philip Aduda na jam'iyyar PDP a zaben.

Kotun har ila yau, ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Aduda saboda rashin gamsassun hujjoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel