Sanata Chukwuka Utazi Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP, Ya Bayyana Dalilansa

Sanata Chukwuka Utazi Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP, Ya Bayyana Dalilansa

  • Jam’iyyar PDP ta sake samun koma baya biyo bayan murabus ɗin ɗaya daga cikin manyan mambobinta da suka daɗe a jam'iyyar
  • Sanata Chukwuka Utazi, fitaccen ɗan siyasa daga jihar Enugu, ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar
  • A wasiƙar murabus ɗin da ya miƙa a ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba, ya bayyana cewa aƙidar da ta jawo shi jam'iyyar ta dusashe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Chukwuka Utazi, tsohon Sanatan Enugu ta Arewa, ya miƙa wasiƙar murabus ɗinsa daga PDP tare da sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa aƙiɗun jam'iyyar da aka kafa ta su waɗanda suka ja shi zuwa cikinta, sun dusashe, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta tanadi hukunci domin raba gardama a tsakanin Gwamna Abba da Nasiru Gawuna

Sanata Chukwuka Utazi ya fice daga PDP
Sanata Chukwuka Utazi ya raba gari da jam'iyyar PDP Hoto: Senator Chukwuka Utazi
Asali: Facebook

Bayan ya wakilci mazaɓar sanatan tun daga shekarar 2015 zuwa 2023, ya mika wasiƙar murabus ɗinsa ga Cif Robert Ezeagu, shugaban jam'iyyar PDP na gundumar Nkpologu, ƙaramar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Enugu, a ranar Lahadi 5 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, wani ɓangare na wasiƙar murabus ɗin Sanata Utazi na cewa:

"Ina sanar da yin murabus ɗin kasance mamba a jam'iyyar PDP wacce na samu damar kasancewa mambanta tun daga lokacin da aka kafa ta a shekarar 1998."
"Dalili kuwa shi ne waɗancan aƙidun da suka ja ni zuwa jam’iyyar sun ɓace ɓat, wanda hakan ya sanya bani da wani zaɓi da ya wuce illa na bar jam'iyyar na samu wata jam'iyyar wacce za ta ba ni damar bayar da gudunmawa ta domin cigaban ƙasa."
"Saboda haka ina yi muku fatan alheri yayin da kuke cigaba da yin aiki tuƙuru domin cigaba da rayuwa halin da ake ciki yanzu. Na gode da fahimtar ku da haɗin kai da kuka ba ni har ya zuwa yanzu."

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan kujerar dan majalisar APC a jihar Edo

Tsohon Sanatan ya zabi ya ƙi bayyana shirinsa na siyasa a nan gaba.

PDP Ta Rasa Kaso 85% Na Magoya Bayanta

A wani labarin kuma, wani babban jigo a jam'iyyar Labour Party (LP), ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta rasa kaso 85% na magoya bayanta.

Katch Ononuju, ya yi ikirarin cewa jam'iyyarsa ta gaje sama da kashi 85 na mutanen da suka saba kaɗa wa jam'iyyar PDP kuri'unsu duk zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel