Shahada: Yadda Wani Dan Jihar Enugu Ya Cira Tsoro Ya Musulunta

Shahada: Yadda Wani Dan Jihar Enugu Ya Cira Tsoro Ya Musulunta

Sunday Remijius, wanda yanzu ya koma Abubakar, ya fito daga karamar hukumar Udenu ta jihar Enugu, kudu maso gabashin Najeriya.

A wannan hira da yayi da jaridar Daily Trust, ya bada labarin yadda ya karbi Musulunci da halin da ya shiga sakamakon haka.

Ya fito daga dangin kiristoci mabiya darikar Katolika masu tsananin tsauri, Abubakar wanda ya kammala karatun tattalin arziki, daga Kwalejin Ilimi ta Jihar Nasarawa, kuma ya samu aiki a babban kantin zamani na Shoprite da ke Abuja a matsayin mai sayar da kayayyaki.

Amma haduwarsa da wani abokin aikinsa ya ja shi zuwa Musulunci. Wannan matakin ya janyo masa samu raunuka hadi da sama masa karfe a kafa sakamakon irin hare-hare da 'yan uwansa suka kai masa kan sai ya bar addinin.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

A cikin wannan hirar, ya bayyana irin kalubalen daya fuskanta kan shigarsa addinin Musulunci, da irin gwagwarmayar da ya yi da iyalansa, da kuma kukan neman agaji, da dai sauransu.

Yaya aka yi ka zama musulmi?

Na karbi addinin Musulunci ta hanyar wani abokin aikina a lokacin da nake aiki a Shoprite da ke Apo, Abuja. Sunansa Ibrahim kuma halayyarsa ya sa na zama Musulmi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kantin Shoprite yana ɗaukar mutane daga wata jiha kuma a tura su wata jiha don gogewa. An dawo ni daga Abuja zuwa Kano amma na hadu da Ibrahim lokacin da aka tura shi Abuja daga Kano.

Ina da wanda suke aiki a kasa na kusan su 23 a lokacin kuma wasu daga cikin shuwagabbaninmu suna yankar Naira 2000 daga cikin albashinmu duk wata mu kuma bamu sani ba, hakan ya faru tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani Jirgin Sama Ɗauke da Mutane Ya Yi Hatsari, Ya Zarce Cikin Kogi

Ibrahim ne a matsayin da masu yanke mana albashin yake da yazo sai muka ga ba haka ba. Da muka tambayaeshi ya haka?, sai yace addininsa ya hana shi cin hanci da rashawa. Na yi tunani indai halinsa haka yake to ina so in kasance cikin addinin.

Yaya matarka ta sami labarin musuluntar ka?

Muna aiki tare a kantin Shoprite tare da ita, tayi fushi sosai da ta lura na canja addini. Duk da cewa tun farko bana so ta san na canza addini.

Amma watarana ta ganni na fito daga masallacin da muke da shi a ofis, sai ta tambayeni me na je yi a can? Shine na fada mata ‘Ni Musulmi ne yanzu’. Sunanta Helen.

Ta ce ba za ta taba shiga Musulunci ba, ta kira danginta suka zo Abuja daga Jihar Nasarawa. Wannan ya faru ne a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

Duk tunaninsu wani ya tilasta min muslunta. Lokacin ya zo daidai da hutuna na shekara sai na sai na yi amfani da damar na tafi Jihar Enugu tare da matata.

Saboda na musulunta, ya sa dangina suka bar Jihar Nasarawa suka koma gida, wai sabida na jawo musu abun kunya, musamman mahaifina mai rike da sarautar gargajiya.

Abubakar
Shahada: Yadda Wani Dan Jihar Enugu Ya Cira Tsoro Ya Musulunta Hoto: @Daily_Trust
Asali: Twitter

Yaya za ku kwatanta abin da kuka fuskanta da iyayenku a matsayinku na musulmi?

Abu ne na tashin hankali wanda ba a iya misaltanshi, musamman ga mahaifina. Yana da wuya ya yarda cewa zan iya zama musulmi kuma na kasance.

Amma mahaifiyata da ƙanwata, wadda ita ce ta ƙarshe a gidanmu, suna sona sosai. Bayan musulunta, idan na rasa sallah ba na ji daɗi ba har sai na rama ta sannan zan yi farin ciki da kwanciyar hankali.

Wata rana Ina yin sallar magrib lokacin ina karanta suratul Fatiha a fili, kwatsam sai naji wani bugu a bayana, Lokacin da na juya, nag a wasu ne daga cikin dangina dauke da katako da ƙarfe da duk abin da za su iya samu.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Na yi kokarin fada da su saboda ni mutum ne mai karfin gaske, amma ina su biyar ne, sun fi karfinna sun doke ni sosai har na suma, sun so su kashe ni, amma Mahaifiyata ce ta hana su ta kwanta a kanta a kaina.

Lokacin da na farfado, na ga cewa ba zan iya tsayawa ba kuma hannayena da kafafuna sun karye. Da farko dai an kai ni wani asibiti da ke Enugu inda na kwanta na tsawon wata shida. Hannuna da kafafuwana sun sami matsala.

Duk lokacin da na yi ƙoƙari na yi tafiya, zan ji kamar kashina na motsi ko kuma naji alamar zai motsa. Na yi shiri na zo Asibitin Dala da ke Kano don samun kulawa ta musamman bisa shawarar Ibrahim.

A can ne aka saka karfe a cikin kafata. Kudina duk ya kare a magani sabida albashi na kusan N200,000 in ka hada harda alawus. Ofis din mu sun ba ni watanni shida amma na shafe kusan shekara guda da makonni biyar ba tare da cikakkiyar lafiya ba, to daga nan ne na rasa aiki a Shoprite. An ƙaunace ni sosai a wajen aiki na, suna son maidamin da aikina amma sabida yanayi bazai yiwu ba

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya yi nadi mai muhimmanci, ya ba wani dan Katsina mukamin babban sakatare

Nawa ne kudin aikin naka?

Kimanin N420,000. An yi min tiyata sau biyu. Bayan ta farko, bayan ƙafata ta shanye, ta da baya ne kuma aka sa ka karfe dan kafar ta daidaita.

A lokacin da ka shiga cikin wannan halin ƙuncin, shin ka sami wani taimako daga danginka?

A'a, sai mahaifiyata da take so na da kuma take ganin nine mai laifi. Duk da bata ba ta ji daɗin zama na musulmi ba, ta dai ban goyon baya lokacin da ta fahimci suna so su ɗauki rai na.

Shin ko ka tuntubi al'ummar musulmin Enugu?

Ni kadai ne Musulmi dan kabilar Igbo a daukacin karamar hukumata, ban da wadanda suka zo Fatauchi. Akwai wani masallaci da nake zuwa na yi sallah daga baya mahukuntan masallacin suka sanar da 'yan sanda halin da ake ciki na yunkurin kasheni.

Amma mahaifina sabida matsayinsa na babban mutum yayi ’yan sandan barazana . Ya ce saboda ni yake so ya koma Nasarawa kuma Ya ce da su “ni ne dansa na farko, to indai ina son zaman lafiya sai dai na bar addinin muslunchi.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Na ce masa ba ni ne na zabi Musulunci ba, Allah ne ya datar dani dashi. Lokacin da nai kokarin debe kayana daga gidan, Ya fada min baza su kara maraba da ni a matsayin dan gidansu ba ha sai na bar musulunchi.

Shugaban yan sandan karamar hukumar ya ban shawara da na bai garin zuwa wani. Amma Mahaifina ya gargade shi da kada ya tsoma baki a cikin wannan lamarin, kada hakan ya haifar da wani rikici.

Wani Bahaushe ya ba ni Naira 50,000, wani kuma ya ba ni Naira 20,000 da dai sauransu. Dole yasa na tafi amma na karbe yata yar shekara bakwai.

Yaya aka yi ka zo Ilorin kuma yaya kake rayuwa

Wani Bahaushe ne da na hadu da shi a Enugu, wanda ya taba sayar da nama a Ilorin, ya shawarce ni da in dawo Ilorin watakila na fi samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a nan.

Kara karanta wannan

Rudani yayin da Gwamna El-Rufai ya yafewa wasu fursunoni hudu saboda wani dalili

Na samu Wani musulmin kirki da ya ba ni masauki, wani Bahaushe kuma ya ce min in ringa karbar abinci kullum. Ina taimakawa fasinjoji da dora musu kaya a cikin mota (lodi) tunda ina kusa da tashar da take lodin Kano, Kaduna da Niger, da sauran jihohin arewa musamman ma lokacin da kafata bata ciwo.

Shin kuna magana da dangin ku?

Mahaifiyata da 'yar autar mu kadai muke Magana dasu a halin yanzu. Akwai wani lokacin da kanwata Lovina ta zo gidana ta gan ni ina barci.

Kur’anina mai fassara wanda nake yawan karantawa kafin in kwanta barci ta ganshi a kasa sai ta fara karantawa. Ya yi daidai da lokacin da mahaifina ya shigo ciki, ihunsa ne ya sa na tashi daga baccin dana ke.

Kayi nadamar musuluntar ka?

Abin da kawai ji a raina shine dangina. Ina matukar son mahaifiyata kuma ranar da za ta fi farin ciki ita ce ita ma ta karbi Musulunci. Hakan zai kara zaburar da wasu da dama su bi sahun na. Amma na san yawancin ’yan uwana ba za su so hakan ya faru ba. Idan na sa jalabiya a can Enugu, mutanena za su yi mini kallon ban san abin da nake yi ba. Suna ganin wani abu marar kyau ko abin kunya.

Kara karanta wannan

Wata Fatima Abubakar Ta Zuba Wa Mijinta Guba a Abinci, Tace Ta Tsani Aure a Rayuwarta

Wane taimako kuke nema yanzu?

Taimakon da nake nema shine game da kafafuna, dasa karfe ya shafeta. Wani lokaci nakan zauna a kasa don yin addu'a.

A wasu lokuta, nakan yi kuka da addu'a Allah ya taimake ni. Wani lokaci, ina mamakin ace shin ni ne mutum na farko da ya fara musulunta.

Lovina ta taba tambayata cewa idan ta musulunta, shin ita ma za ta shiga cikin irin ciwon da nake ciki. Idan ina da hanya, da na kusantar da ita kusa da ni. Ta kammala karatunta a Jami’ar Jihar Nasarawa. Ina kokarin lallashinta ne domin nasan In Sha Allahu zan zama silar karbar addinina a gidana.

Nawa ne kudin aikin?

Likitan a Dala ya ce N120,000 kuma na yi kokarin tara kudin ta hanyar sayar da wayata daya tilo da nake da ita a yanzu akan N11,000. Ba ni da kowa kuma. Na sayar da Mercedes dina 190 a lokacin da aka min aikin farko. Na so in yi shiri siyar da babur ɗina amma na san ƙannena suna amfani da shi. Dole na manta da ra'ayin saboda ba na son wani abu da zai rushe farin cikin iyalina.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel