Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan Jihar Enugu

Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan Jihar Enugu

  • Kotun koli ta kori karar da APC da dan takararta na gwamna a zaben ranar 18 ga watan Maris,a jihar Enugu, Uche Nnaji, suka shigar kan PDP da Peter Mbah
  • Mai shari’a Tijani Abubakar na kotun koli ya yanke cewa Nnaji da APC sun shigar da kara mara inganci sannan basu gabatar da cikakken hujja don tabbatar da ikirarinsu
  • Da farko kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Enugu da kotun daukaka kara sun yi watsi da karar da Nnaji da APC suka shigar kan Gwamna Mbah da PDP

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Enugu - Kotun koli ta yi watsi da karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta a zaben gwamnan jihar Enugu, Uche Nnaji, suka shigar a gabanta.

APC da Nnaji dai suna kalubalantar nasasar Peter Mbah na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka yi, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kamfanin Samar Da Wutar Lantarki Na Jihar Kebbi Ya Kama Da Wuta

Kotun koli ta kori shari'ar APC da dan takararta kan gwamnan Enugu
Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan Jihar Enugu Hoto: Uche Nnaji
Asali: Twitter

Dalilin da yasa kotun koli ta kori karar APC kan PDP a Enugu

Da yake hukunci a ranar Juma’a, 15 ga watan Satumba, kwamitin mutum biyar na babbar kotun ya riki cewa tawagar lauyoyin APC da Nnaji sun shigar da kara mara tushe balle makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, kwamitin ya ce masu karar sun kasa gamsar da babbar kotun dalilin da zai sa a saurari karar da suka daukaka wanda bai da inganci.

A hukuncin da kotun ta yanke, Mai shari’a Tijani Abubakar ya ce tun da aka gano bayanin wadanda ke karar ba shi da inganci, rashin ingancin ya kuma shafi karar da wanda aka shigar da karar a kansa.

Ya ci gaba da yin watsi da bayani da karar da masu karar suka daukaka.

Hukumar INEC Ta Gaza Kare Nasarar Gwamnan PDP a Gaban Kotun Zabe

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: An Zo Kan Gwamnoni, Ƙotun Zaɓe Zata Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP

A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gaza kare nasarar gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, na jam'iyyar PDP a gaban kotun zaɓe.

Rahoton The Nation ya nuna cewa INEC ta gaza kare tuhumar da ɗan takarar gwamna na Labour Party, Chijioke Edeoga, ya yi a Kotu cewa an tafka magudi a zaɓen gwamnan Enugu 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng