Matsin tattalin arziki
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta taimaki akalla mutane miliyan 20 a kasar nan ta tsare-tsaren da ta fitar don saukaka wahalar rayuwa ta hanyar tura masu kudi.
Tsohon shugaban Majalisar Tarayya, Hon. Yakubu Dogara ya kare Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan cire tallafin man fetur inda ya ce ba laifinsa ba ne.
Masu shirya zanga zanga ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 sun rubuta wasiƙar neman ƴan sanda sun samar masu ingantaccen tsaro a lokacin da suka fito.
Masu shirya zanga-zangar ranar 1 Oktoba, 2024 na matsa kaimi wajen tattaro kawunan matasan kasar nan domin nuna adawa da yadda ake tafiyar da gwamnati.
Darajar kudin Najeriya ta kara faduwa a farashin gwamnati da kasuwar fayan fage ta ƴan canji ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024, Dala ta koma N1,9l680.
Gwamnatin Tarayya ta ware makudan kudi har N24bn domin tallafawa gidaje fiye da 900 a jihohin Najeriya 36 da birnin Tarayya, Abuja domin rage radadi.
A wannan labarin za ku ji yadda gwamnatin tarayya ta sake ba yan Najeriya hakuri kan halin kunci da wasu daga cikin manufofinta su ka tsunduma jama'a.
Sakataren gwamnatin tarayya ya lissafa manyan ayyukan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a Najeriya. Sakataren ya lissafa karin albashi cikin ayyukan.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kara daukar tsauraran matakai domin kara samun kudin shiga. Bola Tinubu zai kara bude kofofin haraji domin habaka tattali.
Matsin tattalin arziki
Samu kari