Dan takara
‘Dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Gombe a Jam’iyyar NNPP, Auwal Isiyaku Seiko, ya maka jam’iyyar a gaban babbar kotun jihar saboda batun takara a zaben 2023.
Za ku ji alkawuran da Rabiu Kwankwaso ya yi wa Yan Najeriya a takardar manufofinsa. An fara ne daga hadin kai da kawo zaman lafiya zuwa bin doka da tsarin mulki
Rabiu Kwankwaso ya kaddamar da manufofinsa, zai maida hankali a kan harkar ilm, yace zai tsawaita wa’adin jarrabawar JAMB kuma ya magance rashin zuwa makaranta
Shugaban matasan jam’iyyar APC na Najeriya yana sa ran za su lallasa PDP a jihar Adamawa, duk da nan ne mahaifar Atiku Abubakar mai neman takara a PDP a 2023.
Maganar da Dr. Iyorchia Ayu ya yi na hana mutum tsayawa takara ya jawo masa suka daga CUPP. Imo Ugochinyere yana ganin shugaban jam’iyyar yana neman kashe PDP.
Bola Tinubu mai takaran shugaban kasar ya bayyana yadda suka yi da shugaban kasa da abin da ya sa ya dauko Sanata Kashim Shettima da rikicin samun tikiti a APC.
A karshen makon jiya ne aka ji labari Jagororin Afenifere sun warware mubaya’ar da Shugabansu ya yi wa Peter Obi, sun ce Bola Ahmed Tinubu za a zaba a 2023
Gwamna Nyesom Wike ya maida martani ga jawabin da aka ji shugaban jam’iyyar PDP ya yi, yace idan Iyorchia Ayu ya isa, ya karbe takarar 'Yan PDP a Jihar Ribas.
Buba Galadima yace akwai shirin da ake yi da nufin a hana BVAS aiki a zaben 2023. 'Dan siyasar yace Sanata Kabiru Gaya ya kama kan shi da ya shiga talabijin.
Dan takara
Samu kari