Osinbajo Ya Zauna da Hadimansa, Ya Fada Masu Wanda Za Su Marawa Baya a Zabe

Osinbajo Ya Zauna da Hadimansa, Ya Fada Masu Wanda Za Su Marawa Baya a Zabe

  • Yemi Osinbajo ya umarci Hadimansa da suke cikin kwamitin PCC su marawa Bola Tinubu baya a 2023
  • Masu aiki a ofishin Mataimakin shugaban kasa za suyi bakin gwargwado domin Tinubu ya lashe zabe
  • Hadimin Mai girma Muhammadu Buhari, Ajuri Ngelale ya bayyana wannan matsaya a Twitter

Abuja - Mai girma mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya umarci mukarrabansa suyi wa jam’iyyar APC aiki a zabe mai zuwa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya yi wannan bayani da ya yi magana a shafinsa na Twitter a ranar Lahadin da ta wuce.

Ngelale a matsayinsa na kakakin kwamitin takarar Tinubu-Shettima yace Yemi Osinbajo ya bukaci hadiman na sa su goyi bayan Bola Tinubu.

Akwai wasu daga cikin masu aiki da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo da sunansu ya fito a cikin kwamitin kamfen APC a 2023.

Kara karanta wannan

Karshen jita-jita: APC ta fadi aikin da matar Osinbajo ke yi don ganin Tinubu ya gaji Buhari

A zaman da ‘dan takaran shugaban kasa watau Bola Tinubu ya yi da Osinbajo, an tsaida magana cewa hadimansa za su marawa APC baya.

Ana yada labaran bogi

Mista Ngelale ya yi wannan bayani ne a matsayin raddi ga masu rade-radin cewa mataimakin shugaban kasa bai tare da APC a zaben badi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Osinbajo da Tinubu
Bola Tinubu da Yemi Osinbajo Hoto: @AjuriNgelale
Asali: Twitter

Daily Post ta rahoto Hadimin shugaban kasa yace jama’a suyi watsi da jita-jita da ke akasin wannan.

Osinbajo ya jaddada wannan lokacin da ya hadu da hadimansa wadanda suke cikin PCC duk da bai cikin kwamitin yakin neman shugaban kasar.

Jawabin Ajuri Ngelale

“Ya kamata a fahimci cewa a taron da aka yi yau, Mai girma Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo ya karfafi dukkanin ma’aikatansa da suka yi dace, suka shiga kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu a 2023, suyi bakin kokarinsu ba tare da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Sha Alwashin Yi wa Tinubu Gagarumin Kamfen

Ayi watsi da sabanin wannan.”

- Ajuri Ngelale

Dazu kun samu labari Dele Momodu ya yi dogon rubutu ya caccaki Asiwaju Bola Tinubu bayan ya fito da manufofin takararsa, yace satar basira ya yi.

Jigon na jam’iyyar PDP yace ‘dan takaran shugabancin kasar na APC ya wanke manufofinsa ne daga wajen MKO Abiola wanda ya yi takara a zaben 1993.

Asali: Legit.ng

Online view pixel