APC tayi waje da Minista, Tsohon Gwamna, da Wasu Daga kwamitin zaben Tinubu

APC tayi waje da Minista, Tsohon Gwamna, da Wasu Daga kwamitin zaben Tinubu

  • A sabon jerin wadanda za su taya APC yakin neman zaben shugaban kasa, babu sunan Rauf Aregbsola
  • Baya ga Ministan harkokin cikin gidan kasar, babu tsohon gwamnan Enugu, Chimaroke Nnamani
  • Dama an yi ta korafi da aka ga sunan Sanatan na jam’iyyar adawa a cikin kwamitin yi wa APC kamfe

Abuja - Jam’iyyar APC ta cire Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbsola daga kwamitin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.

Premium Times tace baya ga tsohon gwamnan na jihar Osun, a sabon jerin ‘yan kwamitin da aka fitar, babu sunan Sanatan Enugu, Chimaroke Nnamani.

A jerin farko da aka fitar, Aregbesola da wasu tsofaffin gwamnoni suna cikin wadanda za su yi wa Tinubu aikin jawo mutane daga kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

An Yi Watsi Da Sunan Rarara a Kwamitin Kamfen Din Tinubu

Yanzu dai babu sunan Ministan wanda sabani ya shiga tsakaninsa da tsohon mai gidansa watau Bola Tinubu a kan tazarcen magajinsa, Gboyega Oyetola.

An cire Chimaroke Nnamani

Chimaroke Nnamani tsohon Gwamna ne wanda ‘dan jam’iyyar adawa ta PDP ne, ganin Sanatan a cikin ‘yan kwamitin da farko, ya jawowa PCC maganganu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wancan lokaci, Bayo Onanuga ya yi kokarin bayyana abin da ya sa aka ga sunan Chimaroke Nnamani duk da Atiku Abubakar yake goyon-baya a zaben 2023.

'Yan takaran 2023
'Yan takaran Shugaban kasan APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

The Cable tace surutun jama’a ya yi tasiri wajen sauyin da aka samu a kwamitin yakin zaben.

Har ila yau, rahoton yace APC ta cire sunan Sanata Orji Uzor Kalu daga kwamitin PCC. Kalu ya yi gwamna a jihar Abia a lokaci daya da Bola Tinubu.

A jerin farko da Hon. James Faleke ya fitar, akwai sunan Orji Uzor Kalu a cikin wadanda za su taya jam’iyyar APC kamfe a zaben shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Sunayen da Aka Kara da Wadanda Aka yi Watsi da su a Kwamitin Neman Takarar Tinubu

Wani wanda aka fahimci babu sunansa shi ne Kassim Afegbua wanda tsohon kwamishina ne a jihar Edo, da farko yana goyo bayan Atiku Abubakar.

Kwanakin baya aka ji labari Kassim Afegbua ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Yanzu bai cikin wadanda za su taya Bola Tinubu yin kamfe.

Sabon jerin 'yan kwamitin kamfe

A jiya kuka ji labari jam’iyyar APC ta fadada 'Yan kwamitin zaben shugaban kasa bayan Gwamnoni da ‘Yan NWC sun koka da jerin farko da aka fitar.

An karawa Abdullahi Adamu matsayi a kwamitin kamfe, amma har yanzu Muhammadu Buhari ne shugaban kamfe, babu sunayen wasu manya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel