Jihohi 6 Mafiya Yawan Masu PVC Bayan INEC Ta Cire Sunan Mutum Miliyan 2.7

Jihohi 6 Mafiya Yawan Masu PVC Bayan INEC Ta Cire Sunan Mutum Miliyan 2.7

  • Hukumar INEC tace mutane miliyan 93.5 aka tabbatar da cewa za su iya kada kuri’arsu a zaben 2023
  • Wadanda suka nemi sabon katin zabe sun kai mutum miliyan 12.29, amma an yi watsi da sunayen wasu
  • A halin yanzu Jihohi irinsu Legas, Kano da Ribas sun fi kowa yawan wadanda za su kada kuri’a a Najeriya

Abuja - Hukumar INEC mai gudanar da zabe na kasa, ta cire mutane 2,780,756 daga cikin wadanda suka yi sabon rajistar katin zabe a Najeriya.

Premium Times tace shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi wannan bayani da ya yi zama da jam’iyyun siyasa ranar Laraba a Abuja.

Mahmood Yakubu yace da farko mutum 12,298,944 aka yi wa rajistar CVR, amma INEC ta goge mutane 2,780,756 (22.6%) saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa CBN Zata Sauya Wasu Takardun Kudaden Najeriya

Dalilan da ya sa aka yi waje da fiye da mutum miliyan 2.7 daga rajistar zaben sun hada da karancin shekaru da yin rajista fiye da sau daya.

INEC tace a zaben 2023 da za ayi, mutane miliyan 93.5 za su kasance suna da katin PVC a hannunsu.

Jihohin da suka yi zarra

Binciken da jaridar Punch tayi, ya nuna Legas, Kano, Kaduna, Ribas, Katsina da Oyo sun fi kowane jihohin yawan masu katin zabe a Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

INEC.
Shirin taron INEC da Jam'iyyun siyasa Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Legas na da 7.57%, Kano ta tashi da 6.34%, Kaduna na da 4.65%, Ribas kuwa 3.77%, Katsina ta samu 3.76% sai jihar Oyo ta na wakiltar 3.51%.

Wadannan jihohi shida sun tattara mutum miliyan 27.68 na wadanda suke da rajista. Hakan yana nufin jihohin suke da kusan 30% na PVCs.

A Legas an yi wa mutum 7,075,192 rajista, sai a Kano ana da 5,927,565, a Kaduna kuwa akwai 4,345,469, yayin da aka samu 3,532,990 a Ribas.

Kara karanta wannan

Darektocin da Aka Kora daga APC Sun Zargi Shugaban Jam’iyya da Wawurar N3bn

Jihohin da ke biye a baya su ne Katsina mai mutane 3,519,260 da kuma 3,275,045 a jihar Oyo. Masu zabe a birnin tarayya Abuja sun kai 1.5m.

Alkaluman Yanki-yanki

Idan aka bi yanki-yanki, Arewa maso yamma na da mutane miliyan 22.7. A jihohin Kudu maso yamma akwai rajistar mutum miliyan 17.93.

Kudu maso kudu na da miliyan 14.4, ana da mutane miliyan 13.8 a Arewa ta tsakiya, sai 12.5m da 10.9m a kudu maso gabas da Arewa maso gabas.

INEC za ta gyara zabe - Victor Ndoma-Egba

A jiya kun ji labari tawagar APC National Integrity Movement ta ziyarci tsohon Sanatan Najeriya, kuma jigo yanzu a jam’iyya mai mulki.

Sanata Victor Ndoma-Egba ya nuna yana goyon bayan cigaban da hukumar INEC ta fito da su wajen shirya zabubbukan 2023 kamarsu BVAS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel