Mai Neman Mulkin Najeriya a PDP Ya Tona Inda Bola Tinubu Ya ‘Sato’ Manufofinsa

Mai Neman Mulkin Najeriya a PDP Ya Tona Inda Bola Tinubu Ya ‘Sato’ Manufofinsa

  • Dele Momodu ya yi dogon rubutu ya caccaki Asiwaju Bola Tinubu bayan ya fito da manufofin takararsa
  • ‘Dan siyasar yace ‘dan takaran shugabancin kasar na APC ya wanke manufofinsa ne daga wajen MKO Abiola
  • A cewar Momodu, babu abin da Gwamnatin APC ta tabuka illa jawo rashin ayyukan yi da talauci a al’umma

Abuja - Mawallafin mujallar nan ta Ovation watau Dele Momodu, ya yi martani a game da takardar manufofin ‘dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Asiwaju Bola Tinubu mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ya gabatar da manufofin da yake da shi idan ya yi dacen samun mulki a 2023.

The Cable ta rahoto Dele Momodu yana mai cewa takardar manufofin na Tinubu mai shafi 80, ba daga ko ina aka dauko shi ba sai a wajen MKO Abiola.

Kara karanta wannan

Osinbajo Ya Zauna da Hadimansa, Ya Fada Masu Wanda Za Su Marawa Baya a Zabe

Marigayi Alhaji MKO Abiola ne ya yi kamfe mai take da ‘Fata’ a shekarar 1993 a lokacin da ya nemi shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar SDP.

An sato takardar Abiola a 2023

A wani dogon rubutu da yayi a ranar Lahadi, The Guardian ta rahoto Momodu yace ‘dan takaran ya wanke manufofin Abiola ne a matsayin alkawuransa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Momodu ya fada, babu wani bambancin kirki tsakanin manufofin Abiola da Tinubu wanda ya fito neman shugabanci bayan shekaru 20.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya gabatar da manufofin takara Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Momodu wanda ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP yace da wannan wanki, Bola Tinubu ya raina hankali da tunanin ‘Yan Najeriya.

‘Dan siyasar yake cewa da ya karanta takardar manufofin da tsohon gwamnan na Legas ya fitar domin zaben 2023, sai ya fahimci giwa ne ya haifi sauro.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

“An san Marigayi MKO Abiola da basira da dagewa, shin za mu tambayi ‘dan takaran APC, da me aka san shi?

- Dele Momodu

A shekaru kusan takwas da APC tayi a mulki, Momodu yace babu abin da aka gani illa karuwar rashin aikin yi, karyewar Naira da tashin farashin kayayyaki.

A haka ne kuma Tinubu yake cewa zai dasa daga inda Muhammadu Buhari ya daura, a rubutunsa, Momodu yace talaucin da APC ta jefa jama’a ne zai karu.

Kasafin kudin 2023

Yayin da ake neman bashi da za a cike gibin kasafin 2023, an ji labari N13,805,814,220 zai tafi wajen biyan tsofaffin shugabannin Najeriya kudin fanshonsu.

Za a raba fanshon ga tsofaffin shugabanni da wadanda suka taba rike mukamin sakatarorin din-din-din da shugabannin ma’aikatan gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel