Takarar 2023: Basarake Ya Zage Yana Yi wa Bola Tinubu da Gwamnan APC Kamfe

Takarar 2023: Basarake Ya Zage Yana Yi wa Bola Tinubu da Gwamnan APC Kamfe

  • Mai martaba Suleiman Ashade ya nuna sai inda karfinsa ya kare wajen tallata Jam’iyyar APC a 2023
  • Oba Suleiman Ashade ya yi kira ga jama’a suyi kokarin ganin Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya
  • Basaraken ya fadawa jama’a wajen wani taro cewa Tinubu da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya dace a zaba

Lagos - Mai martaba Oba Suleiman Ashade ya sha alwashin yi wa Asiwaju Bola Tinubu da Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu aiki a zabe mai zuwa.

Kamar yadda The Nation ta fitar da rahoto, Oba Suleiman Ashade ya yi wannan bayani a wajen wani taro da aka kira domin tanadar katin zabe na PVC.

Suleiman Ashade wanda shi ne shugaban kwamitin da ke kula da wuraren ajiye motoci a Legas ya halarci taron da aka yi a Akesan da ke garin Alimosho.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Basaraken ya yi kira ga al’umma su marawa Bola Tinubu da Gwamna Babajide Sanwo-Olu a zaben shugaban kasa da na gwamnan jihar Legas da za ayi.

Tinubu, Babajide Sanwo-Olu ne zabi - Ashade

A cewar Ashade, ‘yan takaran na jam’iyyar APC ne suka fi cancanta da jama’an Najeriya a yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar tace Mai martaba Ashade ya yi kira ga wadanda suka halarci taron da aka yi, da su tallata ‘dan takaran APC domin ya lashe zaben shugaban kasa.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Gwamna Babajide Sanwo-Olu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“Ina jinjina maku gaba dayanku da kuka mallaki katin PVC. Aikin ya wuce mallakar katin. Yanzu dole ku dage, ku marawa Asiwaju Bola Tinubu da Gwamna Babajide Sanwo-Olu baya.
Ku tallata su ga matanku, mazajenku, makwabtanku, aminanku da mutanenku a duka bangarorin kasar nan, ku fada masu Tinubu ne alherin da Najeriya take jira.

Kara karanta wannan

APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

Ku fada masu nasarorin Legas, susan cewa Asiwaju zai iya, kuma ya shirya kawowa kasar nan irin wannan cigaba.

- Oba Suleiman Ashade

Oluseyi Bamgbose ya jaddada kira

Oluseyi Bamgbose wanda ya yi jawabi a wajen, ya yabawa tsohon gwamnan na jihar Legas, yace mutum ne mara nuna kabilanci, wanda yake tafiya tare da kowa.

Kamar yadda Oluseyi Bamgbose ya shaida, Tinubu a shirye yake ya magance matsalolin da suka addabi Najeriya, yace bai dace a sake zaben tumun-dare ba.

APC ta fadada kwamitin PCC

Kuna da labari jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fadada kwamitin zaben shugaban kasa bayan Gwamnoni da ‘Yan NWC sun koka a kan jerin farko.

An karawa Abdullahi Adamu matsayi a kwamitin kamfe, amma har yanzu Muhammadu Buhari ne shugaban kamfen Bola Tinubu a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel