
Jihar Benue







Gwamnatin jihar Benue ta kulle kamfanonin tsohon gwamna, Samuel Ortom kan zargin kin biyan haraji na makudan kudi inda wasu ke zargin bita da kullin siyasa ne.

Wasu miyagun 'yan bindiga sun hallaka wani shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) a jihar Benue. 'Yan bindigan sun yi masa kwanton bauna ne yana kan hanyr zuwa gida.

Babbar kotun jiha mai zama a Makurɗi ta amince da buƙatar tsawaita umarnin da ta bayat na hana APC rusa kwamitin gudanarwa ƙarƙashin Agaba a jihar Benue.

Jam'iyyar APC ta kasa ta kira taron gaggawa kan rikicin da ya barke a APC a jihar Benue wanda ya shafe sama da shekara. Za a yi taron APC ne a birnin tarayya Abuja.

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya yi watsi da zaben fitar da gwani da tsagin APC mai biyayya ga Philip Agbese ya yi wanda ya ki bin umarnin Abdullahi Ganduje.

Sabon rikici ya kunno a kai a APC reshen Benuwai yayin da tsagin kwamitin shugabancin rikon kwarya na Omale da na bangaren Austin Agada suka fara nunawa juna yatsa.

Za a ji cewa Babban Sufeton kasar nan, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa sun yi nasarar kashe kasungurmin dan ta'adda a lokacin da su ka kai dauki ga dalibai.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta musanta cewa an biya 'yan bindiga kudaden fansa kafin a sako daliban lafiya da aka yi garkuwa da su a jihar Benue.

Korarrun shugabannin jam'iyyar APC a jihar Benue sun garzaya gaban kotu. Shugabannin sun kai karar Abdullahi Umar Ganduje saboda kin bin umarnin kotu.
Jihar Benue
Samu kari