Atiku Abubakar
Shugaban cocin INRI Evangelical, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa za a zaɓi Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar jam'iyyar hadakata a 2027.
Atiku Abubakar ya ce gazawar Bola Tinubu ce ta jawo Donald Trump ya ki gayyatar Najeriya taron kasashen Afrika. Atiku ya ce darajar Najeriya ta zube karkashin Tinubu
Tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika ya karya ikirarin Nyesom Wike da Bayo Onanuga na cewa ya bar APC ya shiga hadakar 'yan adawa a ADC.
Dan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar ADC a zaben 2023, Dumebi Kachikwu ya ce tsagin Mark na shirin tsaida Atiku Abubakar takarar shugaban ƙasa.
Tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya ce kawancen ADC ba shi da ƙarfi ko daidaito don fuskantar Bola Tinubu a 2027, ya ce PDP ce kaɗai ke da karfin takalar APC.
PDP ta musanta umartar 'ya'yanta su shiga ADC, tana mai cewa ita yanzu ta mai da hankali kan dinke barakar jam'iyyar da shirye-shiryen babban taron kasa kafin 2027.
A labarin nan, za ku ji cewa ana hasashen wasu daga cikin manyan da suka taru a ADC domin fatattakar gwamnatin Bola Tinubu za su nemi kujerar shugaban kasa.
Fitaccen ɗan jaridar nan, Dele Momodu ya bayyana cewa babu wani abu ko da tikitin takara ne da zai raba Atiku, Obi da sauran kusoshin haɗaƙa a jam'iyyar ADC.
A labarin nan, za a ji tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya yi zargin cewa yan adawa sun shiga ADC ta hannun baragurbin cikinsu.
Atiku Abubakar
Samu kari