Atiku Abubakar
Yayin da ake taron hadaka a Abuja, tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya fice daga jam’iyyar APC tare da shiga ADC, yana cewa Najeriya na cikin mawuyacin hali.
A kokarin hadakar jam'iyyun adawa, Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai da Dino Melaye sun hallara a birnin Abuja domin kaddamar da jam'iyyar ADC a Najeriya.
An fara samun matsala a haɗakar yan adawa bayan Kungiyar “Concerned Stakeholders of the ADC” ta bayyana damuwa kan nadin sababbin shugabannin a ADC.
Peter Obi ya mika bukatar yin takara wa'adi daya ga gamayyar 'yan adawa a Najeriya. Obi ya ce zai yi takara sau daya ba tare da yin tazarce ba a 2031.
An hana su Atiku dakin taron kaddamar da ADC a Abuja ba zato ba tsammani. 'Yan adawar sun ce ba za su ja da baya ba yayin da suka zargi sa hannun gwamnati.
Ƙungiyar adawa ta Atiku ta zaɓi ADC don doke Tinubu a 2027, tare da naɗa David Mark da wasu ƙwararru a matsayin shugabanni, yayin da take kuma neman rajistar ADA.
Wasu 'yan jam'iyyar ADC a Najeriya sun yi watsi da maganar hadakar 'yan adawa da aka kulla. Sun ce ba a tuntube su ba kafin a yi maganar hadaka don kifar da Tinubu.
Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya ce za su mayar da hankali kan samar ilimi mai inganci da adalci a Najeriya yayin da ya yi jawabin fara aiki a Abuja.
Jam'iyyar APC ta ce 'yan adawa masu kokarin hada kai a ADC ba za su yi tasiri a kan Bola Tinubu ba. Mai magana da yawun APC ya ce su za su yi nasara a 2027.
Atiku Abubakar
Samu kari