Arewa
Gwamnatin jihar Plateau ta sanya dokar hana fita har na tsawon awanni 24 a karamar hukumar Mangu yayin da matsalar tsaro a yankin ke kara kamari.
Gwamnatin jihar Sokoto ta yi Allah wadai tare da barranta kanta da kalaman wani darakta a jihar ga Shehu Usman Dan Fodiyo yayin wani taron siyasa a jihar.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta lashe zabukan dukkan kananan hukumomi 27 da kansiloli 312 a jihar Borno a zaben da aka gudanar a jiya Asabar.
Korarrun 'yan Majalisun jihar Plateau guda 16 da aka rusa zabensu a Kotun Daukaka Kara sun sha alwashin komawa kujerunsu karfi da yaji a gobe Talata.
Akalla mutane uku ne ake fargabar sun mutu bayan da kasa ta zabtare ta fada kansu a lokacin da suke hakar jar kasa a jihar Nasarawa, har yanzu ba a gansu ba.
Kungiyar ACF ta ce ana maida ayyuka zuwa Kudu daga garin Abuja, kuma a ma’aikatar jiragen sama, darektoci 8 daga cikin 40 da aka nada ne kurum daga Arewa.
Muhammad Badaru, ministan tsaron Najeriya ya yaba da irin yadda Umar Namadi ya ɗauko ayyukan alheri a jihar Jigawa yayin ziyarar da ya kai ta farko ranar Asabar.
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da biyan naira dubu 35 ga ma'aikatan jihar don rage musu radadi bayan cire tallafin mai a Najeriya baki daya.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta yi nasarar cafke wani matashi mai suna James Isma'il da zargin kisan kai a Sharada da ke karamar hukumar Gwale a jihar.
Arewa
Samu kari