Arewa
A ranar 14 ga watan Janairu, 2024 kamfanin 'Retail Supermarket Nigeria Limited (RNSL) ya sanar da rufe kantin Shoprite na Kano, tare da fadi dalilin daukar matakin.
Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Abbas Tajudden ya bayyana irin goyon baya da Nasir El-Rufai da Gwamna Uba Sani suka ba shi yayin neman kujerar Majalisar.
A jihar Kano an sha samun kisan gilla wanda ya ke tayarwa jama'a hankali saboda munin kisan, Hausa Legit ta tattaro wasu daga ciki da ake kan shari'arsu yanzu.
Tsohon kwamishinan ayyuka na musamman a gwamnatin Yahaya Bello na jihar Kogi, Kwamared Yahaya Isma'il, ya rasu ranar Litinin da yamma, an masa jana'iza.
Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa da ke kalubalantar zaben Gwamna Sule Abdullahi a jihar wanda ya yi nasara a jam'iyyar APC.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi godiya ga 'yan jihar bayan ya samu nasara a shari'ar zabe a Kotun Koli a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu a Abuja.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (NSEMA) reshe jihar Neja ta bayyana cewa na samu rahoton hatsarin jirgin ruwa a jihar wanda ya rutsa da mutane akalla 100.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da cafke wani matashi da ake zargin ya sace janareton masallacin Juma'a mai amfani da hasken rana a jihar.
Karamin Ministan Tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya amince don yin aiki tare da Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara musamman bangaren rashin tsaro.
Arewa
Samu kari