Dan Arewa Ya Mayar da Wayar Sama da Naira Miliyan 1 Ga Fasinja Bayan Ya Tsinta a Cikin Adaidaitarsa

Dan Arewa Ya Mayar da Wayar Sama da Naira Miliyan 1 Ga Fasinja Bayan Ya Tsinta a Cikin Adaidaitarsa

  • Wani dan asalin jihar Katsina da aka bayyana sunansa da Labahani ya tsinci waya kirar iPhone 13pro Max, ya mayar wa mai ita
  • An ruwaito cewa, Labahani ya dauki wata 'yar kabilar Igbo a adaidaita sahunsa, inda ta mance wayar, wanda ya sashi neman ta don mayar mata
  • Farin ciki maras misaltawa ya lullube mai wayar har ta rungume shi, kuma wannan kyakkyawar dabi'ar ya ja hankalin mutanen Arewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yan Najeriya sun jinjinawa wani matashi dan Arewa mai suna 'Labani', wanda ke sana'ar tuka adaidaita sahu da ya tsinci waya kirar iPhone 13pro Max, kuma ya mayar wa mai ita.

An ruwaito cewa Labahani dan asalin jihar Katsina ne, wanda kuma ya kara haska tsantsar gaskiya da koyarwar addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Buhari ya fadi dalilin da yasa ya ki fito da sakamakon WAEC dinsa a 2015

Dan Arewa ya tsinci iPhone 13 Pro, ya mayar wa mai ita, ta rungume shi don murna
Dan Arewa ya tsinci iPhone 13 Pro, ya mayar wa mai ita, ta rungume shi don murna. Hoto: @Auta_Musa
Asali: Twitter

Labahani ya ki karba kudi daga hannun matar

An ƙiyasta kudin wayar ya kai sama da naira miliyan daya, wanda gaskiyarsa ta saka farin ciki maras misaltawa ga mamallakiyar wayar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ma'abocin shafin Twitter, @Auta_Musa_ ya wallafa labarin matashin a shafinsa, tare da dora hotunan matashin da mai wayar.

Auta Musa ya ce:

"Wata mata 'yar kabilar Igbo ta manta wayarta kirar iPhone 13pro Max a cikin adaidaita sahun wani Labahani, mai makon ya riƙe, sai ya neme ta tare da damka mata wayarta.
"Yana ba ta wayar ya juya ya shiga kekensa ba tare da neman ko sisi daga matar ba."

Auta Musa ya ce matar ta yi - ta yi Labahani ya karbi kudi don nuna godiyar ta amma ya ki karba.

An jinjinawa gaskiyar da Labahani ya nuna

Sai cewa ya yi:

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama makanike da ya tsere da motar kwastoma bayan kawo masa gyara a Legas

"Babu wani dalili da zai saka na rike abin da ba nawa ba, domin addinin Musulunci ya gargade mu akan sarar kayan wani."

Ganin yadda matar ta takura masa tare da saka bakin wasu mutane a wajen, ya sa Labahani ya karbi Ihisanin da ta yi masa.

Auta Musa ya ce abin da Labahani ya yi, abin a yaba ne kuma a yi masa fatan alkairi, la'akari da tsadar wayar.

Hotunan da Auta Musa ya wallafa sun nuna yadda matar ke cike da farin ciki har ta rungume Labahani a tsaye kusa da adadaita sahunsa.

Kalli hotunan a kasa:

Tsohon hadimin Buhari ya jinjinawa gaskiyar Labahani

Jim kadan bayan wallafa labarin Labani da ya mayar da wayar sama da naira miliyan da ya tsinta a adaidaita sahunsa, tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmed ya jinjina masa.

Bashir Ahmed ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

Kara karanta wannan

NSCIA: Malaman musulunci sun koka kan Halin da Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma

"Ina jinjinawa kokarin Labahani dan jihar Katsina kan kyakkyawan aikin da ya yi na mayar da wayar sama da naira miliyan daya da ya tsinta a adaidaita sahunsa.
"Labahani ya kara fito da tsantsar gaskiya da darajar addinin Musulunci, lallai ya cancanci a yaba masa."

Kotu ta garkame matashi bayan gaza biyan bashin banki

A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta samu nasara a wata babbar kotun jihar Bauchi bayan da aka garkame wani matashi da ya karbi bashin banki amma ya gaza biya.

Rahotanni sun bayyana cewa Aminu Yusuf ya karbi bashin naira miliyan 1.6 daga bankin FCMB da nufin bunkasa sana'ar sa, amma a karshe ya cinye kudin, kuma ya ki biyan bashin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel