Gwamnan Arewa Ya Haramta Amfani da Kowane Kalar Babur, Ya Kafa Doka Kan Amfani da Keke Napep

Gwamnan Arewa Ya Haramta Amfani da Kowane Kalar Babur, Ya Kafa Doka Kan Amfani da Keke Napep

  • Gwamnatin Taraba ta haramta hawa babur a Jalingo, babban birnin jihar, ta kafa kwamitin da zai lura da bin wannan doka
  • Haka nan kuma gwamnatin ta ƙayyade lokacin zirga-zirgar Keke Napep daga ƙarfe 6 na kowace safiya zuwa karfe 8 na dare
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar ne zai jagoranci kwamitin wanda ya kunshi hukumomin tsaro da na sufuri reshen jihar Taraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jalingo, jihar Taraba - Gwamnatin jihar Taraba ta haramta amfani da babura kowane iri ne a cikin birnin Jalingo, babban birnin jihar da ke Arewa maso Gabas.

Bayan haka kuma gwamnatin ta taƙaita zirga-zirgar a daidaita sahu tsakanin ƙarfe 6:00 na safiya zuwa ƙarfe 8:00 na dare, kamar yadda Channels tv ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ana jita-jitar Kwankwaso zai sauya sheƙa, wani gwamna ya gana da jiga-jigan APC, ya buƙaci abu 2

Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba.
Gwamnatin Taraba Ta Haramta Hawa Babur a Jalingo, Ta Takaita Keke Napep Hoto: Agbu Kefas
Asali: Twitter

Hakan ya biyo bayan kafa kwamitin da zai lura da tabbatar da hana amfani da babura (Okada) da kuma kula da sabuwar dokar Keke Napep.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin gwamnan jihar Taraba, Aminu Alkali, ne ya jagoranci kafa kwamitin a madadin mai girma gwamna, Agbu Kefas.

Gwamnati ta kafa kwamitin da zai lura

Kwamitin ya ƙunshi kwamishinan rundunar ƴan sandan jihar, CP Joseph Eribo, a matsayin shugaban kwamitin tare da hukumar kiyaye haɗurra (FRSC).

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), hukumar sibil defens (NSCDC), Taraba Marshal da shugaban kungiyar sufuri ta kasa (NURTW).

Yayin da shugaban hukumar harkokin cikin gida da ayyuka na musamman ne zai yi aiki a matsayin sakataren kwamitin.

Gwamnatin ta ɗora wa kwamitin alhakin kama duk wanda ya yi kunnen ƙashi a waɗannan dokokin da aka sanya kana ya gurfanar da shi a gaban kotun tafi da gidanka.

Kara karanta wannan

Kamar Kano, mutane sun yi cincirondo wurin tarban gwamnan APC bayan hukuncin Kotun Ƙoli

Haka nan kuma duk baburan da aka kama da Keke Napep da aka kama sun karya wannan dokar za a rugurguza su.

Tinubu ya gana da tawagar CAN

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin ƙungiyar kiristoci ta ƙasa CAN a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Duk da Tinubu ya lashe zaben shugaban ƙasa da tikitin Musulmi da Musulmi, ya yi alƙawarin kafa gwamnatin kowa da kowa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel