Abun Bakin Ciki
An tabbatar da mutuwar matar nan da ta bai wa ilimi gudummuwa a Najeriya kuma mai rike da sarautar Yeye Mofin ta Legas, Leila Fowler a jiya Lahadi, 7 ga Satumba.
Wasu hatsabiban 'yan bindiga sun sace matar shugaban jam'iyyar APC a karamar hukumar Patigi ta jihar Kwara, da 'yarsa, a ranar Lahadi da daddare.
Rikicin addini ya barke a Bangladesh wanda ya yi sanadin mutuwar wani, ‘yan sanda sun fara farautar masu tsattsauran ra’ayi bayan sun tono kabarin malami Nurul Haque
Wata dattijuwa mai suna Victoria ta ce yan sanda sun hallaka danta mai suna Moses da ya je gidan gwamna don isar da saƙon Ubangiji da yi masa wa'azi.
Mummunar ambaliya ta mamaye kauyuka bakwai a Taraba bayan saukar ruwan sama mai yawa, inda kogin Benue ya yi ambaliya tare da lalata gidaje da gonaki.
Kwamishinan hukumar da'ar ma'aikata kuma tsohon dan Majalisar Wakilai, Hon. E.J. Agbonayinma ya karyata labarin cewa guba aka sanya wa Arase a abinci.
Rundunar ‘yan sanda a Kano ta gayyaci shugabar karamar hukumar Tudun Wada a jihar, Sa’adatu Salisu kan zargin umartar harbe wasu ma'aikatan kamfani.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jagoran yan ta'adda, Kachalla Abu Dan Barka, da wasu mayaƙansa huɗu sun mutu a harin abokan gaba a karamar hukumar Maru, Zamfara.
Rundunar tsaro a Najeriya ta umarci tsofaffin sojojin da ke zanga-zanga a ma’aikatar kudi da ke Abuja da su bar wurin don bai wa gwamnati damar aiki.
Abun Bakin Ciki
Samu kari