Yadda Gwamna a Najeriya Ya Ci Mutuncin Ciyaman Din Karamar Hukuma a Bainar Jama’a, an Yada Bidiyon

Yadda Gwamna a Najeriya Ya Ci Mutuncin Ciyaman Din Karamar Hukuma a Bainar Jama’a, an Yada Bidiyon

  • Wani shugaban karamar hukumar a jihar Anambra ya ga ta kansa yayin da Gwamna Charles Soludo ya caccake shi a gaban jama’a
  • Gwamnan ya ci mutuncin Pascal Aniegbuna ne kan zargin bari a gina wasu shaguna a bakin hanya ba tare da barin fili ba
  • Gwamnan ya yi barazanar korar Pascal daga kujerar a cikin wani faifan bidiyo idan har bai rushe ginin ba kafin ya dawo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra – Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya caccaki wani ciyaman na karamar hukuma, Pascal Aniegbuna kan rashin kula da aikinsa.

An gano gwamnan a cikin wani faifan bidiyo ya na cin mutuncin ciyaman din a cikin taron jama’a a kasuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba da sabon umarni ga rundunar tsaro bayan kisan sojoji 16, ya yi Allah wadai

Gwamnan PDP ya yi barazana ga shugaban karamar hukuma kan rashin kula da aiki
Gwamna Soludo ya yi barazanar korar ciyaman na karamar hukuma a Anambra. Hoto: Charles Soludo, TheCable.
Asali: Facebook

Wane umarni Soludo ya ba ciyaman din?

Gwamnan ya zargi Pascal ne da barin wani mai gida ya gina katanga har bakin titi ba tare da barin inda mutane za su wuce ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Ododoukwu da ke Okpoko a karamar hukumar Ogabru da ke jihar.

Soludo ya umarci Pascal ya tabbatar ya rushe ginin ko kuma ya kore shi daga mukamin shugaban karamar hukumar.

Gargadin da Soludo ya yi

“Wannan ginin an yi shi tun yaushe? Ya kamata ka rushe shi, idan na sake zuwa nan baka rushe shi ba zan kore ka a mukami, kwata-kwata baka kware ba.”
“Kana gani aka fara ginin amma baka ce komai ba ko rushe shi, ka kawo min wanda ya amince da wannan ginin zan kore shi.”

- Charles Soludo

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya tona asirin inda aka kai daliban da aka sace a Kaduna, bayanai sun fito

Gwamnan ya umarci a rushe dukkan shagunan da ke bakin hanyar saboda samar da hanyar da mutane za su na wucewa.

Za a tsige mataimakin gwamna

Kun ji cewa ana zargin mataimakain gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu da wasu laifuffuka kan zargin tsige shi.

Majalisar jihar ta na zargin Shaibu kan laifuffukan da suka hada da tona asirin gwamnatin jihar da kuma shaidar karya.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Gwamna Soludo da mataimakinsa kan siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel