Abuja
An zargi ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, da kitsa kisan marigayi Bako Angbashim, DPO na karamar hukumar Ahoada ta Gabas.
Jami'in NSCDC da ya yi katobarar 'Oga at the top', Shem Obafiaye ya samu karin girma zuwa mataimakin kwamnadan hukumar a Najeriya bayan shekaru 10.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya roki majalisar dokokin tarayya da ta amince ma'aikatar FCT ta samu naira biliyan 17.2 da aka ware mata a kasafin 2024.
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Dakta Chukwuemeka Ezeife ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 85 a duniya. Ya rasu a Cibiyar Lafiya na Tarayya da ke Abuja.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya fadi bayan kammala bikin ranar haihuwarsa a otal din Transcorp Hilton da ke Abuja a jiya Alhamis.
Tsohon shugaban kamfanin man NNPCL, Dakta Thomas John Maurice ya riga mu gidan gaskiya a yau Alhamis 14 ga watan Disamba ya na da shekaru 84 a duniya.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sallami Kabir Mohammed da Tayyib Odunowo a matsayin shugabannin FAAN da NAMA tare da maye gurbinsu da wasu nan take.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sallami dukkan daraktocin ma'aikatar harkokin jiragen sama kwana daya bayan korar shugaban hukumomin FAAN da NAMA a jiya Laraba.
Yan bindiga sun aikata barna a Abuja bayan sun sace shugaban kungiyar dillalan jaridu ta birnin tarayya Abuja. Miyagun yan bindigan sun bukaci a ba su N15m.
Abuja
Samu kari