Wike Ya Rusa Shahararriyar Kasuwar Kilishi a Abuja, Ya Fadi Dalili

Wike Ya Rusa Shahararriyar Kasuwar Kilishi a Abuja, Ya Fadi Dalili

  • Alkawarin da Nyesom Wike ya dauka na tabbatar da tsaftace babban birnin tarayya Abuja ya fara zama gaskiya sannu a hankali biyo bayan matakin da ya dauka
  • Barazanar Wike ya ritsa da shahararriyar kasuwar nan ta Area 1 yayin da aka rushe shagunan da basa bisa ka'ida a cikin kasuwar, lamarin da ya 'dai'daita yan kasuwa da dama
  • Muktar Galadima, daraktan kula da ci gaban FCTA, ya ce shagunan da wasu gine-ginen da ba sa bisa ka'ida da wuraren ajiye motoci sun sa ba a iya bin hanyar kasuwar

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya sake rusa wata shahararriyar kasuwa a Abuja.

Gwamnatin Wike ta rusa shahararriyar kasuwar kilishi a Abuja
Wike Ya Rusa Shahararriyar Kasuwar Kilishi a Abuja, Ya Fadi Dalili Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Muhammad B Muhammad
Asali: Facebook

A ranar Litinin, 18 ga watan Satumba ne hukumar babban birnin tarayya (FCTA) ta rusa shahararriyar kasuwar Kilishi da ke yankin Area 1 Abuja, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Fusata, Ya Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Matarsa Da Ta Roki Sarakuna a Madadinsa

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa an rushe kasuwar ne a ranar Litinin bayan wata takarda da daraktan kula da ci gaban hukumar FCTA, Muktar Galadima ya aika a ranar Lahadi, 17 ga watan Satumba, a yayin wata ganawa da yan kasuwa da masu shaguna a kasuwar ta Arewa 1.

Dalilin da yasa aka rushe shahararriyar kasuwar kilishi

An yi taron ne domin samun fahimtar juna da yan kasuwa da masu shaguna a yankin kafin a yi rushe-rushen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Galadima ya bayyana cewa za a cire shagunan da basa bisa ka'idan ne domin tsaftace muhallin.

A halin da ake ciki, tun bayan da Wike ya kama aiki a matsayin ministan Abuja, ya sha alwashin tsaftace babban birnin tarayyar da kuma rushe gine-ginen da basa bisa ka'ida.

Kara karanta wannan

Ana zaman dar-dar: Gini ya ruguje kan jama'a, mutum 2 suna can jina-jina a asibiti

Da yake magana kan dalilin rusa kasuwar, Galadima ya ce:

"Yadda kasuwar ke cike da cunkoso da rashin tsafta yana da hatsari ga tsaro da lafiyar yan kasuwa da kwastomomi."

Kungiyar MURIC ta zargi Tinubu da fifita Yarbawa da Kiristoci a nade-nadensa

A wani labari na daban, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha caccaka kan nade-naden mukaman siyasa da gwamnatinsa ta yi, yayin da aka yi masa tuni kan tikitin Musulmi-Musulmi wanda shi da mataimakinsa Kashim Shettima suke shugabanci a kai.

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta bukaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da ganin cewa dukkan yankuna, addinai da sassa sun amfana daga nadin mukaman da gwamnatinsa sannan kada a fifita wata kabila ko addini sama da saura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel