Tinubu Ya Bayyana Cewa Wike Hadiminsa Ne Ba Iya Ministan Abuja Ba

Tinubu Ya Bayyana Cewa Wike Hadiminsa Ne Ba Iya Ministan Abuja Ba

  • Shugaba Bola Tinubu ya zazzaga kalaman yabo ga sabon ministan babban birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike
  • Tinubu ya bayyana cewa Wike ba kawai ministan Abuja ba ne, ya kasance hadiminsa kuma mai goyon bayansa
  • Shugaban ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 14 ga watan Satumba a fadar shugaban kasar da ke Abuja

FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alakar da ke tsakaninshi da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Tinubu ya ce Wike ba kawai ministan Abuja ba ne a wurinshi, hadiminsa ne na musamman wanda ya ke taimaka masa, Legit ta tattaro.

Tinubu ya bayyana Wike a matsayin hadiminsa ba iya minista ba
Tinubu Ya Yabawa Wike Da Irin Mutuncin Da Ke Tsakaninsu. Hoto: Bola Tinubu, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Meye Tinubu ya ke cewa kan Wike?

Shugaban ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 14 ga watan Satumba yayin tarbar wani kwamiti daga jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamnan PDP Da Tawagar Masu Ruwa da Tsakin Jiharsa a Villa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Vanguard ta tattaro cewa, Tinubu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Ajuri Ngelale ya fitar a jiya kamar haka:

“Mai girma ministan birnin Tarayya Abuja ba kawai minista ba ne, hadimi na ne kuma mai goyon baya na.
“Ya ba da gudumawa sosai wurin tabbatar da ci gaban gwamnatin nan, kuma ya kamata ya samu kwarin gwiwa daga jiharsa.”

Tinubu ya fadawa ma su ruwa da tsaki na jihar Ribas cewa ya ji korafe-korafensu na ayyukan raya kasa a yankunansu.

Ya ce korafin na su ya shafi lalatacciyar hanyar Elementary Onne da ta hada da hanyar da ta wuce zuwa matatar Fatakwal.

Wike na tsaka mai wuya kan mukamin Tinubu

Jam'iyya PDP na zargin ministan Abuja, Nyesom Wike da yi wa jam'iyyar zagon kasa.

Wike wanda asalin dan jam'iyyar PDP ne ya bijirewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

Jam'iyyar ta yi barazanar korar shi saboda goyon bayan jam'iyyar APC a zaben watan Faburairu na shugaban kasa.

Matakin da Wike zai dauka kan PDP

A wani labarin, mai sharhi kan lamuran siyasa, Segun Akinleye, ya bayyana cewa ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike na barazanar lalata jam'iyyar PDP.

Akinleye, a wata tattaunawa da Legit, ya yi nuni da rikicin shugabancin jam'iyyar Labour inda Julius Abure da Lamidi Apapa, ke ayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar na kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel