An Tono Yadda Sambo Dasuki Ya Raba Biliyoyin Kudin Makamai zuwa Asusun Bankuna

An Tono Yadda Sambo Dasuki Ya Raba Biliyoyin Kudin Makamai zuwa Asusun Bankuna

  • Wani jami’in Access Bank ya bayyana yadda ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki, ya karɓi kuɗaɗen tsaro a 2015
  • Shaidar EFCC ta ce kamfanonin Jabbama Ada, Jawas Multipurpose da Onile Nigeria sun karɓi kuɗaɗe daga asusun ONSA, ciki har da Naira biliyan biyu
  • A shari’ar karkatar da Naira biliyan 4.6, wanda ake tuhuma sun musanta zargin, yayin da kotu ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 17 ga Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani jami’in banki ya bayyana yadda ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki, ya karɓi kuɗaɗen tsaro daga Babban Bankin Najeriya (CBN).

An raba kudaden da hadin guiwar Ofishin Akanta Janar na Tarayya a shekarar 2015, da yadda aka tura kuɗaɗen ga wasu mutane da kamfanoni.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

An bankado yadda Dasuki ya raba kudin makamai
Tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Source: Twitter

Shaida daga banki ya magantu

Arhyel Mshelia, jami’in kula da bin ƙa’idoji a bankin Access, ya bayar da shaida a gaban Babbar Kotun Abuja, a matsayin shaida ta uku ta masu gabatar da ƙara a shari’ar zargin damfarar kuɗaɗen sayen makamai ta Naira biliyan 4.6 da ta shafe sama da shekaru 10, cewar Premium Times.

Mshelia ya bayyana yadda kuɗaɗen tsaro suka shiga asusun kamfanonin Jabbama Ada Global Services, Jawas Multipurpose Ventures da Onile Nigeria Limited a shekarar 2015.

Ana shari’ar Dasuki tun shekarar 2015 tare da tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa, ɗansa Sagir Bafarawa, tsohon ƙaramin ministan kuɗi, Bashir Yuguda, da kamfanin Dalhatu Investment.

Sambo Dasuki da sauran waɗanda ake tuhuma suna fuskantar tuhume-tuhume 25 da suka haɗa da karkatar da kuɗaɗe, karya amana ta hanyar aikata laifi da karɓar dukiyar sata.

Masu gabatar da ƙara sun zarge su da karkatar da Naira biliyan 4.6 daga asusun ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

Kara karanta wannan

Obi ya bukaci Bola Tinubu ya koma gida ya huta, ya bar maganar takarar 2027

An ce kuɗin an ware su ne domin sayen makamai don ƙarfafa yaƙi da ’yan ta’addan Boko Haram a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, tsakanin shekarun 2014 da 2015.

Yayin da yake duba bayanan asusun ONSA a ranar Talata, shaidar ta shaida wa kotu cewa tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Dasuki, da wani Salisu Abdulmalik Shaibu ne suka kasance masu sa hannun asusun a bankin Access.

Arhyel ya ce a ranar 16 ga Maris, 2015, asusun ya karɓi Naira miliyan 500 daga CBN, sannan aka fitar da kuɗin a ranar 25 ga Maris, 2015.

Haka kuma, an saka Naira biliyan biyar a asusun a ranar 10 ga Afrilu, 2015. A ranar 16 ga Afrilu, an tura Naira miliyan 27 da miliyan 400 zuwa kamfanin Jabbama Ada Global Limited.

Shaidar ta ce Salisu Umar Garu ne mai sa hannun asusun kamfanin Jabbama Ada, kamar yadda Punch ta ce.

Ya kuma bayyana cewa kamfanin Jabbama Ada ya karɓi Naira miliyan 500 a ranar 5 ga Fabrairu, 2015, da kuma Naira biliyan ɗaya a ranar 16 ga Afrilu, 2015 daga ofishin ONSA.

Kara karanta wannan

Wike ya faɗi abin da zai hana Obi zama shugaban ƙasa, ya tuna mummunan halinsa 1

An gano babbar badakala kan kudin makamai
Jami'an hukumar EFCC a bakin aiki. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Source: UGC

Yawan kudin da kamfanoni suka karba

Daga asusun Kwamitin Raba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC) da ke ƙarƙashin Ofishin Akanta Janar na Tarayya, kamfanin ya karɓi Naira miliyan 38 da miliyan 25 a ranakun 6 da 7 ga Janairu, 2015, da kuma Naira miliyan 55 a ranar 5 ga Fabrairu, 2015.

A cewar shaidar, kamfanin Onile Nigeria Limited, wanda Tom Ikimi ne mai sa hannun asusunsa, ya karɓi Naira miliyan 200 da miliyan 100 daga ONSA a ranakun 9 da 18 ga Fabrairu, 2015.

Ya kuma ce kamfanin Jawas Multipurpose Ventures ya karɓi Naira biliyan biyu, a lokacin da lauyoyin waɗanda ake tuhuma suka yi masa tambayoyi, shaidar ta ce bai san dalilin waɗannan mu’amalolin kuɗaɗe ba.

Ya bayyana cewa kamfanin Jabbama Ada yana gudanar da ayyukan kwangiloli na gama-gari, kasuwancin mai da iskar gas, saye da sake sayar da filaye, da harkokin sufuri.

Shaidar ta kuma bayyana cewa an yi wasu musayar kuɗaɗe zuwa hedikwatar tsaro ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Da gaske an fitar da Naira tiriliyan 2.3 don ƙaddamar da kamfen APC a Kaduna? Gaskiya ta fito

Yayin da yake amsa tambayoyin lauyan Yuguda da na kamfanin Dalhatu Investment Limited, James Olatoke, babban lauya mai daraja ta SAN, shaidar ta ce bai san wata alaƙa tsakanin Jabbama Ada da waɗanda yake karewa ba.

Ya kuma bayyana cewa akwai kuɗaɗen da aka tura daga wasu mutane da kamfanoni, ban da ONSA da CBN.

Shaida ta farko, Hamza Abdullahi, wanda ya kasance mataimakin shugaban rundunar musamman ta EFCC da ta binciki zargin damfarar kuɗaɗen sayen makamai a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, ya shaida cewa an gano Naira biliyan 4.633 a asusun kamfanin Dalhatu Investment Limited.

EFCC na ci gaba da shari'ar Dasuki

A baya, an ji cewa karar da EFCC ta shigar da tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, za ta dawo sabuwa.

Hukumar EFCC za ta sake gurfanar da Kanal Sambo Dasuki mai ritaya a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja a ranar Talata.

Sambo Dasuki dai yana fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi zargin karkatar da kuɗin da suka kai N33.2bn da yake ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.